Kasafin kudin 2019: Gwamnatin Buhari zata kakabawa 'yan kasa sabbin haraji don samun kudin shiga

Kasafin kudin 2019: Gwamnatin Buhari zata kakabawa 'yan kasa sabbin haraji don samun kudin shiga

Yayin da hanyoyin samun kudaden shigar gwamnatin tarayya ke ta dada kara tsukewa, Gwamnatin ta shugaba Muhammadu Buhari ta bayyanawa 'yan kasar kudurin ta na bullowa da sabbin dabarun samun kudade daga 'yan kasar domin samun kudaden shiga da za'a aiwatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Wannan dai na kunshe ne a cikin jawabin ministar kudi ta gwamnatin tarayyar, Hajiya Zainab Ahmed lokacin da take yiwa 'yan jarida da ma su ruwa da tsaki jawabi filla-filla a game da kasafin kudin a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kasafin kudin 2019: Gwamnatin Buhari zata kakabawa 'yan kasa sabbin haraji don samun kudin shiga

Kasafin kudin 2019: Gwamnatin Buhari zata kakabawa 'yan kasa sabbin haraji don samun kudin shiga
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wata kasuwa a Arewa ta kama da wuta

Legit.ng Hausa ta samu cewa Ministar kudin ta ce duba da irin yadda gwamnatin bata samu ta aiwatar da kasafin kudin 2018 yadda ya kamata ba saboda rashin kudin, yanzu ya zama dole gare su da su maida hankali wajen bullo da sabbin dabarun samar da kudaden shigar kamar su haraji ga 'yan kasar da dai sauransu.

A wani labarin kuma, 'Yan majalisar wakillai a tarayyar Najeriya sun bayar da umurni ga jami'an yan sandan Najeriya karkashin shugaban su, Ibrahim Idris da su gaggauta cafke daya daga cikin hadiman shugaban Kasar Najeriya mai suna Mista Okoi Obono-Obla.

Shi dai Mista Okoi kamar yadda muka samu, shine matakin na musamman ga shugaban kasar akan harkokin bincike da kai kara a kotu watau senior special assistant to the president on prosecution a turance.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel