Kai ba dan yankinmu bane – Kungiyar matasa ga Atiku

Kai ba dan yankinmu bane – Kungiyar matasa ga Atiku

- Kungiyoyin matasa a karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto sunce ikirarin da Atiku Abubakar ke yin a cewar shi dan yankin ne karya ne

- Atiku dai ya bayyana cewa tushensa daga karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto yake a lokacin kamfen dinsa

- Sun bayyana cewa yayi ikirarin ne kawai don cimma manufar siyasarsa

Wasu gamayyar kungiyoyin matasa a karamar hukumar Wurno da ke jihar Sokoto sunce ikirarin da Atiku Abubakar ke yin a cewar shi dan yankin ne karya ne.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta tuna cewa dan takarar shugaban kasar a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a lokacin gangamin arewa maso gabas a Sokoto a ranar 3 ga watan Disamba ya bayyana cewa tushensa daga karamar hukumar Wurno da ke jihar.

Kai ba dan yankinmu bane – Kungiyar matasa ga Atiku

Kai ba dan yankinmu bane – Kungiyar matasa ga Atiku
Source: UGC

NAN ta ruwaito cewa Wurno gari ne ga Sultan din Sokoto na farko, marigayi Muhammadu Bello, dan Shehu Usman Dan Fodio.

KU KARANTA KUMA: Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki (hotuna)

Da suke mayar da martani ga ikirarin a ranar Juma’a a Sokoto, kungiyar a wani sanarwa na hadin gwiwa dauke da sa hannun Murtala Wurno da Alhaji Kabiru Wurno shugabanin kungiyar manoman shinkafa da na tafarnuwa sunce Atiku bai da alaka da yankin.

Sun bayyana cewa yayi ikirarin ne kawai don cimma manufar siyasarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel