Maku ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a Nasarawa idan ya zama gwamna

Maku ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a Nasarawa idan ya zama gwamna

- Labaran Maku, dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar APGA a jihar Nasarawa yayi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a jihar idan har aka zabe a 2019

- Ya ce zai dawo da zaman lafiya a dukkanin yankuna na jihar cikin kwanaki 100 na farko da zai yi akan mulki

Labaran Maku, dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a jihar Nasarawa yayi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a jihar idan har aka zabe shi a zaben 2019.

Maku, wanda ya kasance tsohon gwamnan sadarwa, yayi wannan alkawari a ranar Juma’a, 21 ga watan Disamba yayinda yake jawabi ga yan gudun hijira a Akon, karamar hukumar Obi.

Maku ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a Nasarawa idan ya zama gwamna

Maku ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro a Nasarawa idan ya zama gwamna
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa zai tabbatar da dawowar zaman lafiya a dukkanin yankuna na jihar cikin kwanaki 100 na farko da zai yi akan mulki.

Maku wanda ya kuma kasance sakataren jam’iyyar APGA ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta wanzar da wani taro na zaman lafiya, hadin kai da kuma tsaro, inda za’a tattauna yadda za’a cimma zaman lafiya a tsakanin mutane.

KU KARANTA KUMA: Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki (hotuna)

Ya kuma bayyana cewa idan aka zabe shi, gwamnatinsa zata tallafawa shugabannin garuruwa da abubuwan sadarwa ta yadda za su isar da rahoton kowani abuda basu aminta da shi ba ga gwamnati don daukar mataki akan lokaci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel