Babbar magana: PDP ta kalubalanci Buhari akan zargin boye N2.6tn na harajin man fetur

Babbar magana: PDP ta kalubalanci Buhari akan zargin boye N2.6tn na harajin man fetur

- PDP ta kalubalanci Buhari da ya fito yayi bayani dalla dalla kan ha'intar 'yan Nigeria sama da N2.6tn ta hanyar boye harajin N48 na man fetur

- Jam'iyyar ta yi zargin cewa da yawan 'yan Nigeria, na biyan wannan boyayyen haraji tun bayan da aka kara kudin man fetur din daga N87 zuwa N145

- PDP, ta kuma zargi Buhari da jam'iyyar APC na yaudarar masu cin gajiyar shirin Anchor Borrowers, na tarawa Buhari N1.2bn, da nufin daukar nauyin yakin zabensa

Jam'iyyar PDP ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fito yayi bayani dalla dalla kan ha'intar 'yan Nigeria sama da N2.6tn ta hanyar boye harajin N48 na man fetur da aka kakabashi ba bisa ka'ida ba.

Jam'iyyar ta yi zargin cewa da yawan matuka motoci a fadin kasar Nigeria, sun kasance suna biyan wannan boyayyen haraji tun bayan da aka kara kudin man fetur din daga N87 zuwa N145.

Sakataren watsa labarai na kasa na jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis, ya kuma zargi Buhari da jam'iyyar APC na yaudarar masu cin gajiyar shirin Anchor Borrowers, na tarawa Buhari N1.2bn, da nufin daukar nauyin yakin zaben tazarcen shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Dogara: Gwamnatin APC ta ci amanar al'ummar Arewa maso Gabas

Babbar magana: PDP ta kalubalanci Buhari akan zargin boye N2.6tn na harajin man fetur

Babbar magana: PDP ta kalubalanci Buhari akan zargin boye N2.6tn na harajin man fetur
Source: UGC

Ya ce jam'iyyar PDP na Allah wadai da duk wani nau'i na cin hanci da rashawa, musamman ma zargin da ake na cewa shugaban kasa Buhari zai kwakulo kudade daga hannun talakawa da ake cin gajiyar shirin Anchor Borrowers, wanda kuma ya sabawa dokokin kudi na kasar.

Haka zalika Ologbodiyan ya yi zargin cewa jami'an fadar shugaban kasa na ci gaba da gudanar da kudurin APC na sayen kuri'u, ta hanyar amfani da shirin TraderMoni. Ya yi zargin cewa suna karbar kaso 10 daga hannun masu cin gajiyar shirin, a matsayin toshiyar baki.

"Don haka jam'iyyar PDP na kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya fito fili, ya bar labe labe, ya fayyace gaskiya kan wadannan zarge zarge da ake yi masa na cin hanci da rashawa, tare da fadar shugaban kasarsa.

"Ya sani cewa 'yan Nigeria sun ja sunyi gum, suna kallon duk abubuwan da ke faruwa. 'Yan Nigeria sun ji karairayi daban daban, sunga yaudara kala kala, wacce wannan gwamnatin mai ci a yanzu ta yi masu, kuma sun shirya tsaf don kawo karshen gwamnatin a zaben 2019."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel