Gwaggwafan lada ga dan Kano da yayi fice a jarrabawar 'yansanda ta bana, tukwuici daga Ganduje

Gwaggwafan lada ga dan Kano da yayi fice a jarrabawar 'yansanda ta bana, tukwuici daga Ganduje

- Gwamna ya sha alwashin bayar da tikwici ga dan asalin jihar ASP Shuaibu Aminu, da ya yi zarra a jarrabawar yan sanda na bana

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da Takobin Girma ga ASP Aminu a bikin yaye dalibai na yan sanda

- A cewar Ganduje wannan abun farin ciki ne kuma ya daukaka martabar jihar

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya sha alwashin bayar da tikwici ga dan asalin jihar ASP Shuaibu Aminu, da ya yi zarra a jarrabawar yan sanda na bana daga makarantar Wudil, jihar Kano.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da “Takobin Girma” ga ASP Aminu a bikin yaye dalibai na yan sanda.

Gwaggwafan lada ga dan Kano da yayi fice a jarrabawar 'yansanda ta bana, tukwuici daga Ganduje

Gwaggwafan lada ga dan Kano da yayi fice a jarrabawar 'yansanda ta bana, tukwuici daga Ganduje
Source: Depositphotos

Da yake Magana da manema labarai bayan bikin, Ganduje yace Aminu wanda ya kammala karatun digiri a fannin lissafi ya daukaka martabar jihar a idanun duniya sannan cewa zai karrama shi akan haka.

“Abun farin ciki ne gare mu sannan kuma muna farin ciki da kasancewar makarantar a Kano. Yaye daliban guda 602 ya kara karfin hukumar yan sandan, wanda yake da matukar muhimmanci ga kalubalen da tsaron kasar ke ciki a yanzu,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Abokan aikina sun yi wa shugaba Buhari ihu ne don bai basu cin hani ba – Hon. Kazaure (bidiyo)

Da yake yaba ma shugaba Buhari akan kalubalantar jami’an yan sandan da yayi kan su guji aikata rahsawa da zai iya lalata sunan hukumar a idanun duniya, gwamnan yace rashawa ya bata sunan hukumomin tsaro matuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel