Kamfanin lantarki na Kaedco, na bin jama'a kudi har N3B a Zamfara kadai

Kamfanin lantarki na Kaedco, na bin jama'a kudi har N3B a Zamfara kadai

- Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna na bin sama da Naira biliyan 3

- Kudaden sun tare ne a shekaru uku da suka gabata

- Hakan na faruwa ne saboda wasu masu amfani da wutar lantarki na ganin ta a matsayin bulus

Kamfanin lantarki na Kaedco, na bin jama'a kudi har N3B a Zamfara kadai

Kamfanin lantarki na Kaedco, na bin jama'a kudi har N3B a Zamfara kadai
Source: Facebook

Injiniya Sabo Abdul, jami'i mai kula da huldar kasuwanci da habaka shi na kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna, KAEDCO yace kamfanin na bin sama da Naira biliyan 3 da mutane masu amfani da wutar ke rike dashi.

Abdul ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyara ga kungiyar 'yan jaridu a ofishin su dake Gusau, a ranar Alhamis.

Yace kudin sun taru ne tun daga fara aikin kamfanin a shekaru uku da suka wuce.

DUBA WANNAN: Assha! Gasar inzali ta kai wani jarumin mata lahira, a zagaye na bakwai

"Wannan abun ya faru ne saboda halayyar wasu masu shan wutar lantarki da suke ganin ta a bulus da kuma rashin biyan kudin wutar, " inji shi.

Ya kara da cewa akwai mutanen da suke jona wutar ba bisa ka'ida ba kuma sukan takura hanyoyin wutar wanda hakan ke kawo matsala ga samuwar wutar.

Yayi bayanin cewa hukumar zata hada guiwa da yan jaridu don wayar da kan mutane wajen gane amfanin wutar da bukatar su dinga biyan kudin wutar.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel