Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki (hotuna)

Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki (hotuna)

- Gobara ta tashi a kamfanin shinkafa na Abakaliki a ranar Alhamis

- Shinkafa da injina da farashinsu ya kai sama da naira miliyan 50 sun kone kurmus

- A cewar shugaban kamfanin Allah ya takaita lamarin saboda agajin gaggawa da hukumar kashe gobara suka kai

Gobara ta tashi a kamfanin shinkafa na Abakaliki a ranar Alhamis yayinda shinkafa da injina da farashinsu ya kai sama da naira miliyan 50 ya kone gurmus.

Daily Trust ta ruwaito cewa taimakon gaggawa da hukumar kashe gobara na jihar suka kai ne ya hana gobarar yaduwa zuwa sauran gine-ginen kamfanin.

Shugaban kamfanin Abakaliki Rice Mill Ltd, Deacon Joseph Ununu, ya tabbatar da lamarin a ranar Juma’a, 21 ga watan Disamba cewa gobarar ta farad a misalin karfe 9 na dare.

Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki

Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki
Source: Depositphotos

Ununu, wanda ya ci gaba da bayyana lamarin a matsayin mai ban al’ajabi ya bayyana cewa wasu muhimman abubuwa sun tsira ne sakamakon agajin gaggawa da masu kashe gobara suka kai.

Yayi bayanin cewa gobarar ya fara ne daga wani gini kadan-kadan inda ya mamaye dukka ginin kafin wani jami’in tsaro da ke bakin aiki ya farga sannan yayi gaggawan sanar da hukumomi.

Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki (hotuna)

Gobara ta lakume shinkafar N50m a kamfanin shinkafar Abakaliki
Source: Depositphotos

KU KARANTA KUMA: Abokan aikina sun yi wa shugaba Buhari ihu ne don bai basu cin hani ba – Hon. Kazaure (bidiyo)

Wani mammalakin shagon shinkafa da ke layi na 13 A, Mista Moses Oboh wanda ke cikin alhinin lamarin ya bukaci gwamnati da ta kawo mashi dauki.

Sakamakon bukuman Kirisimeti, ana ciniki da gaggawan siyan shinkafa a kamfanin shinkafan Abakaliki yayinda ake siyar jakar 25k tsakanin N5,500 da N6,000.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel