Hukumar EFCC ta cafke Mutane 2 da N1bn a filin jirgin sama na jihar Enugu

Hukumar EFCC ta cafke Mutane 2 da N1bn a filin jirgin sama na jihar Enugu

Rahotanni da ke zuwa mana a halin yanzu da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, ta samu nasarar cafke wasu Mutane dauke da zunzurutun kudi na N1bn a filin jirgin sama na jihar Enugu.

Hukumar hana yiwa tattalin arziki ta'annati ta Najeriya watau EFCC, ta samu nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargin su da taka dokokin hada-hadar kudi ta kasa, inda suka shiga hannun jami'an tsro dumu-dumu da zunzurutun kudi na Dalar Amurka miliyan 2.8.

Hukumar EFCC ta cafke Mutane 2 da N1bn a filin jirgin sama na jihar Enugu

Hukumar EFCC ta cafke Mutane 2 da N1bn a filin jirgin sama na jihar Enugu
Source: Facebook

Ababen zargin, Ighoh Augustine da kuma Ezekwe Emmanuel, sun shiga hannu a harabar filin jirgin sama na kasa da kasa na Akanu Abiam da ke jihar Enugu a Kudancin Najeriya.

Hukumar EFCC ta bayyana cewa, miyagun sun shiga hannu dauke da akwatuna biyu makire da Dalar Amurka miliyan 1.4 rike a hannu kowanensu yayin da suke yunkurin sayen tikitin jirgi domin shillawa zuwa jihar Legas.

A yayin da suka ji matsa ta jami'an tsaro, sun amsa laifin su da cewa, sun kasance kan wannan mummunar harka tsawon shekaru shida ta safarar kudi ga wasu sanannun Bankuna a kasar nan.

Sun ce a halin yanzu su na kan hanyar su ne ta cika aikin wani Banki da aka sakaya sunansa da yake yankin sabuwar kasuwar Onitsha a jihar Anambra. Kazalika sun ce sun gudanar da makamancin wannan aiki sau hudu kacal a wannan shekara.

KARANTA KUMA: An kitsa kisan Alex Badeh - Dan Majalisa Chika Adamu ya yi zargi

Kakakin hukumar han yiwa tattalin arziki ta'annati, Mista Tony Orilade, shine ya bayar da shaidar hakan a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai. Ya ce hukumar za ta gurfanar da su gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta samu nasarar cafke wani dan kasar Lebanon, Abbas Lakis, da zunzurutun dukiya ta kimanin N980m a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke garin Abuja inda ya yada zango bayan ya baro jihar Kano akan hanyar sa ta zuwa kasar Lebanon.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel