Tukur Buratai ya kai wa Sojojin Operation LAFIYA DOLE ziyara

Tukur Buratai ya kai wa Sojojin Operation LAFIYA DOLE ziyara

Shugaban hafsun Sojin Najeriya, Lafatana Janar Tukur Buratai, ya kai wata ziyara na musamman wajen Rundunar Sojin Operation LAFIYA DOLE da ke faman yaki a Yankin Arewa-maso-gabashin Najeriya.

Tukur Buratai ya kai wa Sojojin Operation LAFIYA DOLE ziyara

Janar Buratai ya gana da Sojojin Operation LAFIYA DOLE
Source: Depositphotos

Tukur Buratai ya ziyarci Sojojin Najeriya da ke filin daga a Yankin Borno domin kara masu kwarin gwiwa wajen yaki da ‘Yan ta’addan Boko Haram. Wani babban Jami’in gidan Sojin Najeriya ya bayyana mana wannan dazu nan.

Janar Usman Sani Kukasheka ya bayyana mana cewa Janar Tukur Yusuf Buratai ya ziyarci rundunar sojojin kasa na bataliya ta 27 na Rundunar LAFIYA DOLE da ke Garin Buni Yadi a cikin Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Kasar.

KU KARANTA:

Darektan yada labarai na Sojojin kasan yace wannan ziyara da shugaban sojojin ya kai, yana cikin kokarin da babban hafsun Sojin kasan yake yi na ganawa da Jagororin Sojojin kasa domin ganin kawo karshen rikicin Boko Haram.

Kukasheka ya bayyana cewa daga cikin wanda su kayi wa Janar Buratai rakiya akwai manyan Jami’an Sojoji wanda su ka hada da Birgediya Janar CA Apere da kuma shugaban bataliyar da ke Buni Yadi, Birgediya Janar AO Oyedele.

Sauran ‘Yan rakiyar sun hada da manyan Sojoji irin su Birgediya Janar AS Ishaq da kuma babban Jami’in ‘Yan Sanda da ke lura da Rundunar Operation LAFIYA DOLE watau Nicholas Tawani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel