Babu abunda gwamnatin Buhari ta tsinana – Shehu Sani

Babu abunda gwamnatin Buhari ta tsinana – Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya ce har yanzu babu wani ci gaba da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo

- Sani ya fadi hakan yayinda yake tattauna batun kasafin kudin da aka gabatar kwanan nan

-Ya ga wautar yan majalisa da suka yiwa shugaban kasar ihu maimakon kalubalantarsa cikin hikima

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa ha yanzu babu wani ci gaba da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kawo.

Dan majalisan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya ya bayyana hakan a yayinda ya bayyana a wani shirin gidan talbijin din Channelsa na siyasa a yau wato Politics Today.

Babu abunda gwamnatin Buhari ta tsinana – Shehu Sani

Babu abunda gwamnatin Buhari ta tsinana – Shehu Sani
Source: Depositphotos

Sani ya bayyana yayinda suke tattauna kasafin kudin da aka gabatar kwanan nan cewa babu wani ci gaba da gwamnati ta kaw tsakani 2017 da yanzu.

KU KARANTA KUMA: Saboda Buhari ya ki rabawa ‘Yan Majalisa kudi ne su ka rika yi masa wulakanci – Kazaure

Ya kuma bayyana cewa yiwa shugabankasa ihu ba shine hanyar kalubalantar gaskiya ba”.

Sani ya bayyana cewa yan majalisa a majalisun dokokin kasar sun rasa babbar daman a daura shugaban kasar akan turba sannan suka kalubalnci yawan kudin da ya gabatar a ranar gabatar da kasafin kudin 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel