Dogara: Gwamnatin APC ta ci amanar al'ummar Arewa maso Gabas

Dogara: Gwamnatin APC ta ci amanar al'ummar Arewa maso Gabas

- Hon. Yakubu Dogara ya ce gwamnatin jam'iyyar APC mai ci a yanzu ta ci amanar al'ummar shiyyar Arewa maso Gabas

- Kakakin majalisar wakilan tarayya ya kuma bukaci al'ummar shiyyar da su canja gwamnatin a zaben 2019 mai zuwa

- Dogara ya ce zaben ba wai tsakanin PDP da APC bane, zabe ne tsakanin 'yan Nigeria da gwamnatin da ta gaza cika alkawuran da ta daukar masu

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya ce gwamnatin jam'iyyar APC mai ci a yanzu ta ci amanar al'ummar shiyyar Arewa maso Gabas, inda ya bukaci al'ummar shiyyar da su canja gwamnatin a zaben 2019 mai zuwa.

A cewar wata sanarwa daga hadiminsa ta fuskar watsa labarai Turaki Hassan, Dogara wanda ya yi jawabi a Gombe, a taron kaddamar da yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP a shiyyar Arewa maso Gabas, inda ya ce "Har yanzu akwai Boko Haram, hasalima babu wani lokaci a mulkin PDP da aka taba kashe sojoji sama da dari.

"A yau idan kana tafiya a kan titunan mota, akwai yiyuwar kashi 70 na sace ka kafin ka isa inda zaka je. Ta kai a yau ba zaka iya yin tafiya daga Kaduna zuwa Abuja ba, face sai ka bar wasiyya ga iyalanka, domin komai zai iya faruwa. Amma a lokacin mulkin PDP, garkuwa da mutane wani bakon lamari ne a Arewacin kasar nan."

KARANTA WANNAN: Yan kauyen Zamfara sun kashe mutane biyar dake taimakawa barayin mutane

Dogara: Gwamnatin APC ta ci amanar al'ummar Arewa maso Gabas

Dogara: Gwamnatin APC ta ci amanar al'ummar Arewa maso Gabas
Source: Twitter

Ya bukaci al'ummar shiyyar Arewa maso gabas da su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada kuri'arsu ga jam'iyyar PDP, domin ci gaban shiyyar, yana mai cewa, "mu al'ummar shiyyar Arewa maso Gabas muna da abubuwan yi da yawa a zaben nan. Wannan zaben ba wai tsakanin PDP da APC bane, ba wai tsakanin Alhaji Atiku Abubakar da shugaban kasa Muhammadu Buhari bane, zabe ne tsakanin 'yan Nigeria da gwamnatin da ta gaza cika alkawuran da ta daukarwa jama'ar, musamman ma daga shiyyar Kudu maso Gabas.

"Muna da hukumar raya shiyyar Arewa maso Gabas, wacce muka sa ran zata fara aiki don farfado da shiyyar, sai dai ba hakan ta kasance ba, har yanzu gwamnatin bata samar da shuwagabannin hukumar ba. Sama da shekaru 3 muka shafe muna roko tallafi daga kasashen waje don ganin wannan hukumar ta Arewa maso Gabas ta fara aiki, amma abun takaici, gwamnatin tarayya taki yin komai akai."

Kakakin majalisar wakilan tarayya, ya yi nuni da cewa, gwamnati mai ci a yanzu ta ci amanar al'umar Nigeria ta fuskar kare rayukan da dukiyoyinsu, yana mai jaddada cewa duk da irin zarge zargen da akeyi, harkar tsaro tafi inganci a lokacin mulkin PDP.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel