‘Yan Majalisa sun batawa Najeriya suna a Duniya – ‘Daliban Najeriya

‘Yan Majalisa sun batawa Najeriya suna a Duniya – ‘Daliban Najeriya

Kungiyar NANS tayi kira ga Majalisar Tarayya su ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda wulakanci da tazortar sa da su kayi a lokacin da ya gabatar da kundin kasafin kudin shekara mai zuwa.

‘Yan Majalisa sun batawa Najeriya suna a Duniya – ‘Daliban Najeriya

‘Daliban Najeriya sun nemi Majalisa ta nemi afuwar Buhari
Source: Depositphotos

‘Daliban Najeriya da ke lemar NANS sun yi kira ga ‘Yan Majalisar Najeriya su nemi afuwar Shugaba Buhari saboda a dalilin ci masa mutuncin da aka yi gaban Duniya. Wani babban Jami’in Kungiyar NANS din ya bayyana wannan.

Kungiyar ta NANS tayi tir da wannan abin kunya da Majalisar tayi. Azeez Adeyemi wanda shi ne Jami’in yada labarai na ‘Daliban Kasar nan ya nemi ‘Yan Majalisa su rika girmama shugabanni tare da yin abin koyi a bainar Jama’a.

KU KARANTA: Kasafin 2019: Shugaba Buhari zai sa dukiyoyin Barayin Gwamnati a kasuwa

A cewar Adeyemi, ‘Yan Majalisar da su ka rika yi wa Shugaba Buhari ihu, sun ci mutuncin Najeriya saboda banbancin su na siyasa. Adeyami yace bai kamata ana nuna banbancin Jam’iyyar siyasa wajen harkar cigaban kasa ba.

‘Daliban na Najeriya sun bayyana cewa su na yi wa ‘Yan Majalisar kallon abin koyi kafin su yi wannan danyen aiki. Adeyami ya nemi shugabannin Majalisar su yi maza su ba Shugaba Buhari hakuri na ci masa mutunci da aka yi.

Bayan ‘Daliban na Najeriya sun nemi Majalisa ta nemi afuwar Shugaban kasar, an kuma yi kira ga ‘Yan Majalisar su fara aikin da ya kamata kan kundin kasafin kudin da aka mika masu kafin lokaci ya kure.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel