Hutun Shekara: Majalisar dattijai ta dake zama har sai 16 ga watan Janairu, 2019

Hutun Shekara: Majalisar dattijai ta dake zama har sai 16 ga watan Janairu, 2019

Rahotannin da Legit.ng Hausa ke samu daga shafin jaridar THISDAY na nuni da cewa majalisar dattijai a ranar ALhamis, ta dage zamanta har sai ranar Laraba, 16 ga watan Janairu, 2019.

Majalisar dattijai ta dage zamanta har sai 16 ga watan Janairu, 2019.

Hukuncin hakan ya biyo bayan wani kudiri kan bukatar hakan da shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Ahmad Lawan ya gabatar, wanda shugaban marasa rinjaye, Sanata Philip Aduda ya goyi baya.

Cikakken bayanin na zuwa...

KARANTA WANNAN: Rikicin cikin gida: Buhari ya bukaci kawo karshen rikice-rikicen APC a fadin Nigeria

Hutun Shekara: Majalisar dattijai ta dake zama har sai 16 ga watan Janairu, 2019

Hutun Shekara: Majalisar dattijai ta dake zama har sai 16 ga watan Janairu, 2019
Source: Depositphotos

Idan ba a manta ba, a ranar Larabar data gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisun dokokin tarayya kasafin kudin kasa na 2019.

Bayan awa daya a tsaye yana kwararo bayanai kan kasafin kudin shekarar 2019 na kudi Tiriliyan 8.83tr, yan majalisan PDP da na APC basu gushe suna iwu a cikin zauren majalisa ba.

Yayinda Saraki ke kokarin kamalla, yan majalisan suna ta ihun 'Sai Baba' wasu na wakokin nuna rashin yarda da Buhari suna wakokin zanga-zanga.

A Karshe a yanke shawara shugaba Buhari ya wuce tunda yan majalisan sun hana kakakin majalisar wakilai magana.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel