2019: Babu dan takarar da za mu marawa baya – Kungiyar Arewa

2019: Babu dan takarar da za mu marawa baya – Kungiyar Arewa

- Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa babu dan takarar shugaban kasa da zata marawa baya a zaben 2019

- Ta dauki matakin ne duba ga cewar mafi akasarin yan takarar yan arewa ne

- Kakakin kungiyar yace za su mayar da hankali wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana cewa babu dan takarar shugaban kasa da zata marawa baya a zaben 2019.

Mukaddashin shugaban kungiyar, Mista Musa Kwande, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 20 ga watan Disamba a yayinda ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Trust Party (PT), Mista Gbenga Hasim, a hedkwatar kungiyar ta ACF da ke jihar Kaduna.

2019: Babu dan takarar da za mu marawa baya – Kungiyar Arewa

2019: Babu dan takarar da za mu marawa baya – Kungiyar Arewa
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa kungiyar ba zata hade da kowace jam’iyar siyasa ko dan takara ba, ciki kuwa harda shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party (PDP).

Kwande yayi bayanin cewa zai zama rashin adalci idan jam’iyyar ta amince da wata jam’iyyar siyasa ko wani dan takara saboda mafi akasarin yan takarar daga arewa ne kuma yaya yankin.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Buhari da Osinbajo na shirin fara kamfen na gida-gida

Yace maimakon marawa wani dan takar baya, kungiyar zata zamo a tsakiya sannan ta mayar da hankali wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kan yankin arewacin kasar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel