Yadda yajin aikin ASUU zai shafi zaben 2019 - INEC tayi bayani

Yadda yajin aikin ASUU zai shafi zaben 2019 - INEC tayi bayani

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU keyi zai shafi shirye-shiryen da hukumar tayi game da babban zaben 2019.

A ranar 5 ga watan Nuwamban 2018 ne ASUU ta shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda rashin cika alkawurran da ke cikin wani yarjejeniya da kungiyar da gwamnati suka rattaba hannu a kai a Satumban 2017.

A ranar Alhamis ne Kwamishinan INEC na kasa kuma ciyaman din yada labarai, Festus Okoye ya bayyana damuwarsa kan irin matsalar da yajin aikin na ASUU zai iya janyo wa a kan zaben wajen wani taron wayar da kan al'umma.

Yadda yajin aikin ASUU zai shafi zaben 2019 - INEC tayi bayani

Yadda yajin aikin ASUU zai shafi zaben 2019 - INEC tayi bayani
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Yiwa Buhari ihu: Iyeyenku basu baku tarbiya ba - Gwamnan APC ya zagi 'yan majalisa

INEC za ta dauki ma'aikatan wucin gadi fiye da miliyan daya ciki kuma har da malaman jami'o'in gwamnatin tarayya, 'yan yiwa kasa hidima (NYSC), da daliban jami'o'in gwamnatin tarayya amma Okoye ya ce za a iya fuskatar tangarda idan ba a dage yajin aikin ba.

Ya ce, "Ba zai taba yiwuwa ba 'yan yiwa kasa hidima su cika guraben ma'aikatan wucin gadi da INEC ke bukata, a wasu jihohin fiye da 70% na ma'aikatan wucin gadin daliban jami'o'in gwamnatin tarayya ne.

"Saboda haka, yajin aikin ASUU zai kawo cikas sosai ga babban zaben 2019. Muna kira da gwamnatin tarayya da ASUU suyi gaggawan sulhuntawa saboda kare mutuncin da kima Najeriya da 'yan Najeriya.

"Yana da muhimmanci daliban jami'a su kasance suna makarantunsu a kalla wata guda kafin ranar 16 ga watan Fabrairun domin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya. Suna da muhimanci ga INEC kuma rashin su zai kawo cikas ga hukumar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel