An kitsa kisan Alex Badeh - Dan Majalisa Chika Adamu ya yi zargi

An kitsa kisan Alex Badeh - Dan Majalisa Chika Adamu ya yi zargi

Za ku ji cewa, daya daga cikin mambobin majalisar wakilan Najeriya, Chika Adamu, ya yi zargin cewa, kisan tsohon shugaban hafsin dakarun tsaro na sojin Najeriya, Air Chief Marshal Alex Badeh, wata kitimurmura ce da aka kitsa ta.

Adamu mai wakilcin shiyyar jihar Neja a karkashin inuwa ta jam'iyyar mai mulki ta APC, ya bayar da shaidar hakan ne cikin zauren majalisar wakilai yayin zaman da ta gudanar a jiya Alhamis.

Dan Majalisar ya ce, kisan tsohon shugaban hafsin dakarun sojin Najeriya babban rashi ne ga al'ummar jihar Adamawa da kuma kasa baki daya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, furucin Adamu ya biyo bayan cecekucen da ya haure ne a zauren majalisar dangane da yiwa lamarin tir gami da Allah wadai.

An kitsa kisan Alex Badeh - Dan Majalisa Chika Adamu ya yi zargi

An kitsa kisan Alex Badeh - Dan Majalisa Chika Adamu ya yi zargi
Source: Facebook

Ya kuma bayyana damuwarsa gami da fargaba dangane da yadda kashe-kashe da zubar da jinin al'umma ya zamto ruwan dare sakamakon rashin ingataccen tsaro a fadin kasar nan.

Cikin nasa jawaban, Toby Okechukwu, dan majalisa mai wakilcin shiyyar Enugu a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP, ya zargi hukumomin tsaro dangane da tabarbarewar al'amurra a cikin kasar nan.

KARANTA KUMA: Rashin aikin yi a tsakanin al'umma ci gaba ne ga Najeriya kuma ribace ga gwamnati na - Buhari

Majalisar yayin zaman da kakakin ta ya jagoranta, Honarabul Yakubu Dogara, ta nemi sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris da kuma shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya na DSS, Yusuf Bichi, akan su gaggauta daura damarar bankado makasan makasan marigayi Alex Badeh.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, marigayi Alex Badeh, ya yi kacibus da ajali akan hanyar sa ta dawowa da gona cikin kauyen Gitata da ke jihar Nasarawa, inda 'yan ta'adda suka bindige shi har lahira tare da Direban sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel