Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 5 a Zamfara

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 5 a Zamfara

- Yan sandan Zamfara ta tabbatar da kisan mutane biyar a kauyen Gidan Halilu da ke karamar hukumar Birnin-Magaji da ke jihar

- Kakakin yan sanda ya ce ana gudanar da aikin bincike da sintiri a yankin a yanzu haka don guje ma sake afkuwar lamarin

- Shehu wanda yace zaman lafiya ya dawo yankin ya roki mazauna dasu ci gaba da lura sosai sannan su kawo rahoton duk wani motsi da basu aminta dashi ba

Rundunar yan sandan Zamfara ta tabbatar da kisan mutane biyar a kauyen Gidan Halilu da ke karamar hukumar Birnin-Magaji da ke jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da yayi a Gusau.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 5 a Zamfara

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutane 5 a Zamfara
Source: Depositphotos

Kamfanin dillacin labaran Najeriya ta ruwaito cewa gawawwaki biyar aka gano yayinda wani mutun daya ya samu rauni.

An dauki gawawwakin zuwa wani asibiti da ke Birnin Magaji yayinda likitoci ke kula da wanda ya samu raunin.

Kakakin yan sanda ya ayyana cewa ana gudanar da aikin bincike da sintiri a yankin a yanzu haka don guje ma sake afkuwar lamarin.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Buhari da Osinbajo na shirin fara kamfen na gida-gida

Shehu wanda yace zaman lafiya ya dawo yankin ya roki mazauna das u ci gaba da lura sosai sannan su kawo rahoton duk wani motsi da basu aminta dashi ba ga ofishin yan sanda akan lokaci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel