2019: Abin da ke bata mani rai game da Najeriya inji Peter Obi

2019: Abin da ke bata mani rai game da Najeriya inji Peter Obi

‘Dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar PDP, Peter Obi, ya bayyana abin da yake bata masa rai game da Najeriya. Obi yayi wannan jawabi ne lokacin da ya zanta da manema labarai a Garin Abuja jiya.

2019: Abin da ke bata mani rai game da Najeriya inji Peter Obi

'Dan takaran PDP a 2019 Peter Obi yayi tir da Gwamnatin APC
Source: Depositphotos

Peter Obi ya koka game da yadda Matasan kasar ke fama da rashin abin yi, ‘Dan takarar yace rahoton da aka fitar na cewa sama da mutane miliyan 87 ba su da abin yi, yana bata masa rai. Obi yace idan aka dauki wasu matakai za a samu sauki.

Obi yake cewa duk da akwai manoman shinkafa har mutane miliyan 15 a Najeriya, shinkafa cigaba da tsada maimakon a samu rangwame a Najeriya. Obi yace Gwamnatin Buhari ta yi shimfidar banza wajen gina tattalin Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa mu ke fama da yawan rashin aikin yi – Buhari

Tsohon Gwamnan ya nuna cewa duk lokacin da ya tuna cewa akwai miliyoyin mutane da ke cikin wani hali na ha’ula’i a Najeriya, sai wannan abu ya bata masa rai. Obi dai ya saba sukar tsarin tattalin arzikin wannan Gwamnatin.

Kafin nan ‘Dan takarar ya gana da kungiyoyi masu zaman kan-su inda yake cewa kudin da Gwamnati ta ke warewa ilmi da kiwon lafiya yayi kasa amma kuma an sake ware makudan kudi domin biyan tallafin man fetur a kasafin 2019.

Mista Obi yayi Allah-wadai da yadda Gwamnatin Buhari ta ke daukar kudi daga bankin masana’antu watau BOI tana rabawa ‘yan kasuwa N10, 000 kacal a maimakon a rika tunanin yadda za a gina Najeriya ta zama tayi nisa a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel