Kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar kamar takarda ce da babu rubutu a ciki - Saraki

Kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar kamar takarda ce da babu rubutu a ciki - Saraki

- Bukola Saraki, ya bayyana kasafin kudin kasar na 2019 da shugaban kasa Buhari ya gabatarwa majalisun dokoki na tarayyar kasar, a matsayin wani kundi maras kima

- Saraki ya bukaci 'yan Nigeria da su cire ransu daga samun wata kyakkyawar makoma daga kasafin da Buhari ya gabatar ko da kuwa majalisun sun amince da shi

- Saraki, ya yi nuni da cewa shugaban kasar bai zayyana hanyoyin da za a samu kudaden da za a kaddamar da kasafin ba

Babban daraktan yakin zaben da takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Bukola Saraki, ya bayyana kasafin kudin kasar na 2019 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisun dokoki na tarayyar kasar, a matsayin wani kundi maras kima.

Saraki ya bukaci 'yan Nigeria da su cire ransu daga samun wata kyakkyawar makoma daga kasafin da shugaban kasar ya gabatar ko da kuwa majalisun sun amince da shi ya zama doka.

Ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa tsakanin dan takarar shugaba kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, da kungiyoyin fararen hula (CSOs), a daren ranar Alhamis, a birin tarayya Abuja.

KARANTA WANNAN: Saraki ya roki kotu ta dakatar da ma'aikatan NASS daga tsunduma yajin aiki

Kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar kamar takarda ce da babu rubutu a ciki - Saraki

Kasafin kudin 2019 da Buhari ya gabatar kamar takarda ce da babu rubutu a ciki - Saraki
Source: Depositphotos

Saraki, a cikin jawabinsa na bude taron, ya yi nuni da cewa kasafin kudin kasar da Buhari ya gabatar a ranar Laraba, baya kunshe da kididdiga mai kyau ga makomar kasar, haka zalika bai zayyana hanyoyin da za a samu kudaden da za a kaddamar da kasafin ba.

"A ranar Laraba, gaba dayanmu mun saurari bayani kan kasafin kudin kasar na 2019. Wannan kasafi ne da babu kyakkyawar makomar 'yan Nigeria a cikinsa, ko a cikin kididdigar kudaden zaka san cewa akwai talauci, idan har aka yi adalci, za aga cewa babu abunda yayi saura daga kudaden haraji da ake tattarawa. Don haka ina makomar kasar take kenan?

"Ya zama wajibi a samar da wata hanyar mafita, wannan ne muke fata kamar yadda a yammacin yau muka zanta da dan takarar shugaban kasa da mataimakinsa, ba wai maganar adawa bace. Ba wai zamuyi zabe kan son zuciya ba, muna so mu zabi abunda yafi dacewa da kasar baki daya."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel