Kungiyar Buhari da Osinbajo na shirin fara kamfen na gida-gida

Kungiyar Buhari da Osinbajo na shirin fara kamfen na gida-gida

- Kungiyar Buhari/Osinbajo kan zaben 2019 sun yanke shawarar fara kamfen din gida-gida a fadin Najeriya don tabbatar da tazarcen su

- Ana sanya ran shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo za su kai kasar mataki na gaba

- Ya bukaci sauran magoya bayan kungiyar da su hada hannu don tabbatar da nasarar Buhari da Osinbajo, inda yace Najeriya ta samu tarin naasarori a shekaru uku da suka gabata

Kungiyar Buhari/Osinbajo kan zaben 2019 sun yanke shawarar fara kamfen din gidaida a fadin Najeriya don tabbatar da tazarcen Shugaban Kasa Muhammdu Buhari da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ake fatan za su kai kasar zuwa mataki na gaba.

Kungiyar Buhari da Obasanjo na shirin fara kamfen na gida-gida

Kungiyar Buhari da Obasanjo na shirin fara kamfen na gida-gida
Source: Depositphotos

Shugaban kungiyar na kasa, Hon. Ayuba Musa Birma, yayin da yake Magana a wani taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, 20 ga watan Disamba ya bukaci masu zabe da su tauna madaci, cewa kamfen dinsu zai yi jan hankali akan zaman lafiyakafin, lokaci da kuma bayan zabe.

Birma a wajen taron da ya samu halartan tsohuwar ministar ilimi, Farfesa Chinwe Obaji da Sanata Tunde Anifowose Kelani da sauransu, sun bukaci dukkanin yan takaran da su bi doka ta hanyar guje ma kamfen da zai haddasa kiyayya, batanci da rabuwar kai a tsakanin yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar 'Kwadago ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

Yayinda yake alkawarin tona duk wanda ya siya kuri’u, ya bukaci hukumar zabe da ta guje ma son kai, sannan ta share duk wani hasashe na yan adawa sannan tayi aiki wajen tabbatar da zabe na gaskiya da inganci.

Ya bukaci sauran magoya bayan kungiyar da su hada hannu don tabbatar da nasarar Buhari da Osinbajo, inda yace Najeriya ta samu tarin naasarori a shekaru uku da suka gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel