Rashin aikin yi a tsakanin al'umma ci gaba ne ga Najeriya kuma ribace ga gwamnati na - Buhari

Rashin aikin yi a tsakanin al'umma ci gaba ne ga Najeriya kuma ribace ga gwamnati na - Buhari

Za ku ji cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne cibiyar kididdiga da fidda alkalumma ta Najeriya, National Bureau of Statistics NBS, ta bayyana yadda adadin marasa aikin yi ya tumfaya daga mutane miliyan 3.3 a shekarar 2015 zuwa miliyan 20.9 a bana.

Wannan lamari ya janyo cece kuce gami da babatu maras yankewa da ya ci gaba da gudana akan harsunan al'ummar kasar nan. Yayin da 'yan adawa ke caccakar gazawar gwamnatin Buhari akan haifar da tasirin wannan mummunan koma baya, wasu na hasashen hakan alheri ne.

Ko shakka ba bu shugaban kasa Muhammadu Buhari, na daya daga cikin masu farin cikin wannan al'amari, inda a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa, yawan marasa aikin yi kamar yadda cibiyar NBS ta fitar ya nuna cewa gwamnatin sa ta samu kyakkyawar riba.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin wani 'dan takaitaccen shagali da babban bankin Najeriya karkashin shirin bayar da bashi ga manoma na Anchor Borrowers ya shirya a babban dakin taro da ke fadar sa ta Villa a garin Abuja.

Rashin aikin yi a tsakanin al'umma ci gaba ne ga Najeriya kuma ribace ga gwamnati na - Buhari

Rashin aikin yi a tsakanin al'umma ci gaba ne ga Najeriya kuma ribace ga gwamnati na - Buhari
Source: Depositphotos

Ya ke cewa, yawaitar adadi na marasa aikin yi a fadin kasar nan alama ce ta al'ummar Najeriya sun farga wajen gano ainihin haske da kuma yalwar arziki da ke cikin harkokin noma, wanda a baya suka kauracewa yayin da suke cikin rashin sani.

Ya ci gaba da cewa, alkalumman da cibiyar NBS ta fitar farin ciki ne gami da riba domin kuwa sun yi daidai da nasara ta gwamnatin sa wajen cimma kudurorin ta na habaka da inganta harkokin noma yayin karbar mulki a shekarar 2015.

KARANTA KUMA: Buhari ya umarci 'Yan sandan Najeriya kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

Mallam Garba Shehu, babban hadimi na musamman ga shugaba kasa kan hulda da manema labarai da kuma al'umma ya zayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya umarci shugaban cibiyar NBS, Dakta Yemi Kale, akan ya fidda kididdigar yadda yawan marasa aikin yi ta yi tasiri wajen habakar harkokin noma a kasar nan.

A yayin haka, dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Peter Obi, ya jingina rashin kyawawan tsare-tsare na gwamnatin shugaba Buhari ya haddasa koma baya na rashin aikin yi a Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel