Saraki ya roki kotu ta dakatar da ma'aikatan NASS daga tsunduma yajin aiki

Saraki ya roki kotu ta dakatar da ma'aikatan NASS daga tsunduma yajin aiki

- Bukola Saraki da Yakubu Dogara, sun bukaci kotu data dakatar da ma'aikatan majalisar dokokin tarayya daga shiga yajin aikin da suka dauki aniyar farawa

- Sun gabatarwa kotun da wannan bukatar a cikin wata takardar mika bukata ga kotu mai lamba No. NICN/ABJ/360/2018 mai kwanan wata 18 ga watan Disamba, 2018

- Idan za a iya tunawa, kungiyar PASAN sun shiga wani yajin aikin gargadi na kwanaki hudu sakamakon basussukan albashi da suke bi da ya kai kusan N2.7bn

Shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki tare da kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, a cikin wata takardar korafin kara dauke da sa hannun mataimakiyar maga takarda, Barrister Hauwa Yakubu, sun bukaci kotun masana'antu da ta dakatar da ma'aikatan majalisun dokokin tarayyar kasar PASAN daga tsunduma yajin aiki.

A cikin wata takardar mika bukata ga kotu mai lamba No. NICN/ABJ/360/2018 mai kwanan wata 18 ga watan Disamba, 2018, ta bukaci shuwagabannin kungiyar PASAN da wakilansu, da su kauracewa shiga yajin aikin da suka yi dau kurin yi.

KARANTA WANNAN: Hanyoyin da yajin aikin ASUU zai kawo cikas ga zaben 2019 - INEC

Takardar mika bukatar tace: "Bukatar umurni na dakatar da wadanda ake kara/ko masu karesu, musamman ma wakilansu, ma'aikatansu, da su kauracewa shiga yajin aikin da suka dauki aniyar yi, har sai bayan karewar wa'adin bukatar da takardar ta gabatar.

Saraki ya roki kotu ta dakatar da ma'aikatan NASS daga tsunduma yajin aiki

Saraki ya roki kotu ta dakatar da ma'aikatan NASS daga tsunduma yajin aiki
Source: Depositphotos

"Bukatar umurnin kotu na dakatar da kungiyar PASAN, da wakilansu, da ma ma'aikatansu daga baiwa mambobinsu umurnin shiga yajin aiki."

Idan za a iya tunawa, kundiyar ma'aikatan majalisar dokokin tarayyar kasar PASAN sun shiga wani yajin aikin gargadi na kwanaki hudu a ranar Litinin, sakamakon basussukan albashi da suke bi da ya kai kusan N2.7bn.

An dakatar da mambobin PASAN daga shiga cikin harabar majalisar dokokin kasar a ranar Laraba, a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake gabatar da kasafin kudin kasar na shekara ta 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel