Buhari ya umarci 'Yan sandan Najeriya kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

Buhari ya umarci 'Yan sandan Najeriya kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a jiya Alhamis, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gindaya wani muhimmin umarni ga jami'an tsaro na 'yan sanda domin daukar mataki yayin babban zaben kasa na 2019.

A ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar da umarni ga jami'an tsaro na 'yan sanda kan tabbatar da zaman lafiya da tsarkake kasar na daga tarzoma da tashin tashina yayin gudanar da zaben kasa na badi.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban Kasa Buhari ya nemi jami'an tsaro na 'yan akan mikewa tsaye tare daura damara gami da zage dantse domin tabbatar da zaben 2019 ya gudana cikin lumana da kwanciyar hankali.

Buhari ya umarci 'Yan sandan Najeriya kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019

Buhari ya umarci 'Yan sandan Najeriya kan tabbatar da zaman lafiya yayin zaben 2019
Source: Twitter

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayn halartar bikin yaye sabbin jami'an 'yan sanda a jiya cikin Kanon Dabo. Ya ce tabbatar da zaman lafiya yayin gudanar babban zabe nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar 'yan sanda a fadin Najeriya.

Ya ke cewa, dole jami'an 'yan sanda su yi tsayuwar daka wajen haramta duk wata bankaura ko bangar siyasa musamman satar akwati ko cin zarafin Malaman zabe da ire-iren su da ka iya aukuwa tare da haifar da cikas wajen gudanar zabe.

KARANTA KUMA: Ba mu da zabi tsakanin Buhari da Atiku - ACF

Kazalika shugaban kasa Buhari, ya taya murna ga sabbin jami'an tareda gargadin su kan tsayuwa bisa akida ta gwamnatin sa mai manufar wanzar da zaman lafiya cikin kasa baki daya.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari yayin ziyarar sa a jihar Kano ya kuma kaddamar da wasu sabbin ayyuka da gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Ganduje ta kammala.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel