Za a saida kadarorin barayi domin a samu kudin shiga a Najeriya inji Buhari

Za a saida kadarorin barayi domin a samu kudin shiga a Najeriya inji Buhari

- Shugaban kasa Buhari yace za a saida wasu kadarorin barayi da aka karbe

- Wannan zai ba Gwamnatin sa kudin shiga domin yin ayyukan more rayuwa

Za a saida kadarorin barayi domin a samu kudin shiga a Najeriya inji Buhari

Gwamnatin Najeriya za ta sa dukiyar sata cikin kasafin kudin 2019
Source: Facebook

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana shirin da Gwamnatin sa ta ke yi a game da dukiyar da Hukukomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa su ka karbe daga hannun Barayin Gwamnati.

Shugaban kasa Buhari yayi wannan jawabi Ranar Larabar nan da ta wuce a lokacin da ya bayyana gaban ‘Yan Majalisar Tarayyar Wakilai da |kuma Dattawa yana gabatar da kundin kasafin kudin Najeriya na shekarar 2019 da za a shiga.

Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa jama’ar Najeriya su na amfana da kudin da Gwamnatin sa ta karbo daga hannun manyan Barayin Gwamnati. Yaki da rashin gaskiya yana cikin manyan alkawuran da Shugaba Buhari ya dauka.

KU KARANTA: 'Yan majalisar sun ba 'yan sanda umurnin cafke wani hadimin Buhari

Yanzu haka Shugaban kasar yace akwai kadarori wanda su ka shafi gidaje da gine-gine da motoci har da filaye na wadanda aka kama da laifin sata a Najeriya da su ke hannun Hukumomin EFCC da kuma ICPC masu maganin miyagu.

Buhari ya tabbatar da cewa yayi wa Hukukomin magana u saida wadannan dukiyoyi da ke kasa ga masu bukata, domin Gwamnati ta samun kudin kashewa. Buhari yace za a sa kudin da aka samu ne domin yin ayyuka a cikin kasafin 2019.

A baya kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta kasafta wasu kudi har Naira Biliyan 200 a gefe wanda ake tunani sun baro hannun Barayin Gwamnatin Kasar zuwa hannun hukuma cikin kudin da za a kashe a shekarar badi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel