Saboda Buhari ya ki rabawa ‘Yan Majalisa kudi ne su ka rika yi masa wulakanci – Kazaure

Saboda Buhari ya ki rabawa ‘Yan Majalisa kudi ne su ka rika yi masa wulakanci – Kazaure

Fitaccen ‘Dan Majalisar Tarayyar nan na Jam’iyyar APC, Muhammad Gudaji Kazaure ya fayyace dalilin da ya sa ‘Yan PDP su ka rika yi wa Shugaba Buhari ihu a lokacin da ya zo Majalisa domin gabatar da kasafin kudi.

Saboda Buhari ya ki rabawa ‘Yan Majalisa kudi ne su ka rika yi masa wulakanci – Kazaure

Yan PDP su na kokarin hana ruwa gudu a Majalisa - Honarabul Gudaji
Source: UGC

‘Dan Majalisar mai wakiltar mazabar yankin Kazaure da kewaye yake cewa ‘Yan Jam’iyyar hamayya sun tasa Shugaba Buhari a gaba ne saboda rashin bada kudi da yake yi kafin ya aikowa Majalisa da kundin kasafin kudin kasar.

Gudaji Kazaure yace Gwamnatocin baya sun saba bada makudan kudi kafin Majalisa ta amince da kasafin kowace shekara. A cewar sa, Shugaban kasa Buhari ya nuna taurin kai na rashin bada cin hanci ga ‘Yan Majalisar Tarayyan.

KU KARANTA: Gudaji Kazaure ya ba Buhari shawara game da sha’anin Boko Haram

Kazaure ya zargi ‘Yan Majalisun PDP da karbar kudi daga hannun Gwamnatin da ta shude a 2015 kafin su yi na’am da abin da Shugaban kasa yake so. Honarabul Kazaure yace shi kuwa Shugaba Buhari ba zai bari ayi wannan aiki da shi ba.

Hon. Kazaure yace ‘Yan Majalisun sun fara shirya yadda za su wulakanta Shugaban kasa ne tun makonni biyu da su ka wuce saboda ya ki ba su kudi kamar yadda su ka saba gani a baya. Kazaure yace ‘Yan adawan na neman kawo cikas a kasar.

‘Dan Majalisar yace burin ‘Yan PDP da ke Majalisa shi ne su hana a gabatar da kundin kasafin 2019, amma hakan bai yiwu ba. Kazaure ya tabbatar da cewa Abokan aikin sa sun tabbatar masa da cewa Buhari ya ki aiko masu kudin da aka saba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel