Ba mu da zabi tsakanin Buhari da Atiku - ACF

Ba mu da zabi tsakanin Buhari da Atiku - ACF

Ko shakka ba bu a halin yanzu, ba bu wani kwararo da guguwar siyasar ba ta karade ba tare da yada zangon ta a fadin kasar nan, yayin da babban zaben kasa na 2019 bai wuci kwanaki 60 da tabbatuwa ba. Hakan 'yan sanya 'yan siyasa ba bu dare ba bu rana, na ci gaba da kai komo da fadi tashi wajen kwankwashen su na neman goyon bayan daidaikun al'umma, kungiyoyi da kuma cibiyoyi domin cimma nasara yayin fidda zakaran gwajin dafi a 2019.

A yayin ci gaba da abin da aka saba kamar kullum, majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wata babbar kungiyar Arewa, ta Arewa Consultative Forum, watau kungiyar tuntube-tuntube da shawarwari ta Arewa, ta bayyana matsayarta kan zaben 2019.

Kungiyar ACF a jiya Alhamis, ta bayyana cewa, ba da ta wani tsayayyen takarar kujerar shugaban kasa tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Mukaddashin shugaban kungiyar, Alhaji Musa Kwande, shine ya bayar da shaidar hakan yayin da Gbenga Olawepo Hashim, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Trust watau PT, ya ziyarci kungiyar a babban ofishin ta da ke jihar Kaduna.

Gbenga Olawepo Hashim; dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Trust, PT

Gbenga Olawepo Hashim; dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Trust, PT
Source: Depositphotos

Alhaji Kwande ya ke cewa, kungiyar ACF ba ta jinginuwa da kowace jam'iyya ta siyasa, ra'ayi na addini ko kuma akida ta kabilanci, da ta kasance Uwa mabada Mama ga dukkanin 'yan takarar kujerar shugaban kasa da ke fadin kasar nan.

Kasancewar ta mai manufa da kare martabar yankin Arewacin Najeriya, Alhaji Kwande ya kuma bayyana cewa, kungiyar ACF na ci gaba da fafuttikar tabbatar da hadin kai, zaman lafiya da kuma yiwa doka da'a domin ci gaban kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Kungiyar 'Kwadago ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

A sanadiyar wannan kungiyar ACF ta ke jaddada matsayar ta na rashin goyon bayan kowane dan takara a yayin zaben 2019. Sai dai ta ce za ta yi tankade gami da rairaya wajen zaben jagora da kishin Najeriya ya mamaye zuciyar sa.

Jagoran na ACF ya kuma kirayi dukkanin 'yan takarar kujerar shugaban kasa da shugabannin jam'iyyu, akan dabbaka yarjejeniyar zaman lafiya da suka sanyawa hannu karkashin gudanarwa ta jakada kuma shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa, Janar Abdulsalami Abubakar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel