Akwai yiwuwar man fetur ya kare a 2070 – Inji Gwamnatin Najeriya

Akwai yiwuwar man fetur ya kare a 2070 – Inji Gwamnatin Najeriya

Mun samu labari cewa Najeriya na iya wayan gari nan da wasu ‘yan lokaci babu man fetur idan har ba a iya gano wasu sababbin rijiyoyin mai a kasar ba. Hukumar DPR na kasar ta bayyana wannan a Ranar Laraba.

Akwai yiwuwar man fetur ya kare a 2070 – Inji Gwamnatin Najeriya

Karamin Ministan man fetur a Gwamnatin Buhari watau Ibe Kachikwu
Source: Depositphotos

Hukumar da ke kula da arzikin mai a Najeriya, DPR, ta bayyana cewa babu shakka fetur na iya karewa Najeriya nan da shekaru 52 masu zuwa muddin ba a iya gano wasu rijiyoyin mai na dabam da za a cigaba da haka a cikin kasar ba.

DPR ta ke cewa Najeriya tana da ganguna kusan biliyan 37 na danyen man fetur ajiye a kasa, sai dai kuma a dauk rana ta Allah, ana hako ganga 1, 973, 995. Hakan ya nuna cewa kafin shekaru 52 za a iya neman fetur a rasa kaf a Kasar.

KU KARANTA: Buhari ba zai halarci muhawarar 'yan takarar shugaban kasa ba - Saraki

Hukumar ta DPR duk tayi wannan bayani ne a wata takarda da Ma’aikatar man fetur ta fitar kwanan nan inda aka rika lissafo irin nasarorin da aka samu a bangaren na man fetur a Gwamnatin nan ta Shugaba Muhammadu Buhari.

Haka kuma, Najeriya tana arzikin gas wanda ya kusa kai awo na TCF har tiriliyan 2. Daga farkon 2017 zuwa yanzu, abin da Najeriya ta ke da shi na arzikin gas ya karu inji Hukumar bayan an gano wasu sababbin rijiyoyin gas kwanaki.

Jaridar This Day ta rahoto Hukumar tana cewa gas din na Najeriya zai ishi kasar har shekaru 55 masu zuwa. Yanzu haka dai Gwamnatin Najeriya na cigaba da kokarin gano rijiyoyin danyen mai a Arewa maso gabashin Najeriya,

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel