An kama babban kwamandan kungiyar Boko Haram a Legas bayan musayar wuta

An kama babban kwamandan kungiyar Boko Haram a Legas bayan musayar wuta

Umar, daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram da ake zargi da daukan nauyin harin hare-haren bam na Kuje da Nyanya dake Abuja a shekarar 2015, ya shiga hannu.

Kazalika ana zargin kwamandan da kisan jami'an 'yan sanda biyu a ofishin hukumar 'yan sanda na Lugbe da Gwagwalada da kuma jagorancin fashi a bankuna a jihohin Edo da Ondo.

Jam'ian rundunar 'yan sanda ta IRT ne suka kama kwamandan a garin Legas bayan musayar wuta.

Majiyar mu ta ce Umar ya samu tsira da raunuka daga yunkurin kama shi da jami'an 'yan sanda suka yi a Abuja, sati uku da suka wuce. Sai dai, an kama hudu daga cikin yaransa da bindigu 4 samfurin AK-47 da alburusai masu yawa.

An kama babban kwamandan kungiyar Boko Haram a Legas bayan musayar wuta

'Yan sandan Najeriya
Source: Twitter

A cewar majiyar mu, Umar ne ya jagoranci harin da mayakan Boko Haram suka kai gidan yari na Kuje inda har ya rasa daya daga cikin idanunsa. Fursuna fiye da 100 ne suka tsere daga gidan yarin sakamakon harin.

DUBA WANNAN: Rigimar duniya: An kama AIG na bogi da katin ATM 11 a Abuja

A wani labarin na Legit.ng mai alaka da wannan, kun ji cewar a jiya ne dakarun soji suka yi nasarar dakile wani harin kunar bakin wake da wata mata tayi niyyar kaiwa a yankin Mushimari a karamar Konduga a jihar Borno.

'Yar kunar bakin wake, Aisha Modu, ta cilla jigidar bam dinta cikin ruwa bayan ta hango dakarun soji na zuwa, amma dakarun sojin sun yi nasarar tsamo jigidar da Aisha ta wulla cikin tafkin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel