Yadda gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka kasafta kudin shiga na watan Nuwamba

Yadda gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka kasafta kudin shiga na watan Nuwamba

Kamar yadda aka saba a kowane wata, gwamnatin Najeriya ta kan kasafta adadin kudaden shiga da ta samu a tsakanin dukkanin matakan gwamnati da suka hadar da ta tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi. Hakan kuwa ta kasance ga watan Nuwamba da ya gabata.

A yau shafin jaridar Legit.ng ya kawo muku yadda gwamnatin Najeriya a jiya Laraba ta kasafta adadin kudaden shiga na watan Nuwamba a tsakanin matakai uku na gwamnatin kasar nan.

Kididdigar kamar yadda kwamitin rarraba kudaden kasa ya fitar ta bayyana cewa, gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi, sun kasafta Naira Biliyan 812.762 a tsakanin su na kudaden shiga da ta tattara a watan Nuwamban da ya gabata.

Yadda gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka kasafta kudin shiga na watan Nuwamba

Yadda gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka kasafta kudin shiga na watan Nuwamba
Source: Getty Images

Kwamitin ya bayar da shaidar hakan ne yayin zaman majalisar da ya gudanar na watan Dasumba kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Alkalumma sun tabbatar da cewa, cikin wannan kasafi, gwamnatin tarayya ta tashi da N294.12bn, gwamnatin jihohi ta tashi da N186.663bn, yayin da kananan hukumomin kasar nan suka tashi da kimanin N140.78bn.

KARANTA KUMA: 'Dan Majalisa ya jefi Firai Minista da kwai yana tsaka da gabatar da jawabai a zauren Majalisa

Baya ga wannan kasafi, jihohi masu samar da albarkatun man fetur da ma'adanansa sun samu wani kaso na musammam kamar kullum, inda suka tashi da N47.882bn.

Cikin kididdigar da alkalumma suka fitar, gwamnatin Najeriya ta samu makudan kudaden shiga a wannan shekara kamar haka;

Janairu - N635bn

Fabrairu - N647bn

Maris - N628.8bn

Afrilu - N701bn

Mayu - N668.9bn

Yuni - N821.9bn

Yuli - N715bn

Agusta - N741bn

Satumba - N698bn

Oktoba - N788.1bn

Nuwamba - N812.76bn

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a jiya Laraba, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gabatar da kiyasin kasafin kudi na N8.8trn na shekarar badi a zauren majalisar dokoki tarayya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel