Hukumar EFCC ta kama manyan masu fashi ta intanet 10 (hoto)

Hukumar EFCC ta kama manyan masu fashi ta intanet 10 (hoto)

Hukumar yaki da cin hanaci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta cafke wasu gagaruman yan damfara ta yanar gizo, bayan wani aiki a musamman da ta gudanar a yankin Port Harcourt. ta dai kama yan damfarar ne har su goma a sassa daban-daban na yankin.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen Port Harcourt ta kama wasu masu damfarar mutane ta intanet.

An kama su ne a wurare daban-daban a lokuta daban-daban a fadin jihar ta Rivers, Warri (jihar Delta da kuma Asaba a jihar Delta a lokacin wani aiki.

Wadanda aka kama sune Alia Jamike Chinemerem; Ogbiugba Ifeany Henry; Uchanna Cyril; Samuel Obomovo; Israel Ogagaoghene; Israel Diaso; Aghariagbonse Destiny; Aretuemhen Frank, Paul Esibhakpen and Loius Idehen.

Hukumar EFCC ta kama manyan masu fashi ta intanet 10

Hukumar EFCC ta kama manyan masu fashi ta intanet 10
Source: Depositphotos

Bincike ya nuna cewa masu laifin suna damfara ne ta hanyar soyayyar karya inda suke nuna cewa su jami’an rundunar sojin Amurka ne.

An bi diddigin sakonni da dama inda suke nuna su sojojin Amurka ne har aka gano su.

KU KARANTA KUMA: Tsohon gwamnan jihar Niger Aliyu ya zargi APC da shirin magudi a zaben 2019

Daya daga cikinsu, Isreael Diasco yayi nasarar damfarar wata yar Indiya, Promilla Lama makudan kudade. Wani kuma Chinemerem ya bayyana cewa shi ne mai zuwa karban kudin, inda za’a biya shi kaso 30 na kudin da aka damfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel