Buhari ba zai halarci muhawarar 'yan takarar shugaban kasa ba - Saraki

Buhari ba zai halarci muhawarar 'yan takarar shugaban kasa ba - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya yi hasashen cewa shugaba Muhammadu Buhari ba zai hallarci muhuwarar 'yan takarar shugabancin kasa da za a gudanar a ranar 19 ga watan Janairun 2019 ba.

Shugaban majalisar ya yi wannan maganar ne a ranar Alhamis a Abuja a wajen wani taro da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar zai gana da wasu kungiyoyin sa kai.

A cewar Saraki, ya dace duk wani da ke neman shugabancin al'umma ya gabatar da kansa a gabansu kuma ya fada musu irin abubuwan da tsinana musu idan sun zabe shi.

Buhari ba zai halarci muhawarar 'yan takarar shugaban kasa ba - Saraki

Buhari ba zai halarci muhawarar 'yan takarar shugaban kasa ba - Saraki
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Ya ce, "An fada min cewa daya ya yi muhawara kuma kun san yadda ta kaya. Shi kuma na biyun, na tabbata ba zai hallarci muhawarar ba. Ta yaya za gane wanda ya cancanci ya jagorance ku idan ba zai iya fitowa ya fada muku abinda zai aikata ba?

"Wannan lokacin ya wuce. Kasar mu itace abin koyi a nahiyar Afirca kuma wannan ba shine irin darasin da muke son su koya daga gare mu ba.

"Duniya ta canja. Idan kana son ka jagoranci al'umma, dole ne ka fito ka bayyana wa al'umma abinda za ka iya musu kuma ka amsa tambayoyi daga garesu kuma wannan shine abinda muke yi a nan.

"Yau ranar kuce, zamu zauna mu amsa tambayoyin ku. Muna fata idan an kammala wannan taron za ku fahimci cewa wannan shine shugabanin da zasu samar da tsaro a Najeriya; za su hada kan 'yan Najeriya, za su magance talauci su inganta rayuwar 'yan Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel