Yan majalisar tarayya sun ba 'yan sanda umurnin cafke wani hadimin shugaba Buhari

Yan majalisar tarayya sun ba 'yan sanda umurnin cafke wani hadimin shugaba Buhari

'Yan majalisar wakillai a tarayyar Najeriya sun bayar da umurni ga jami'an yan sandan Najeriya karkashin shugaban su, Ibrahim Idris da su gaggauta cafke daya daga cikin hadiman shugaban Kasar Najeriya mai suna Mista Okoi Obono-Obla.

Shi dai Mista Okoi kamar yadda muka samu, shine matakin na musamman ga shugaban kasar akan harkokin bincike da kai kara a kotu watau senior special assistant to the president on prosecution a turance.

Yan majalisar tarayya sun ba 'yan sanda umurnin cafke wani hadimin shugaba Buhari

Yan majalisar tarayya sun ba 'yan sanda umurnin cafke wani hadimin shugaba Buhari
Source: Depositphotos

KU KARANTA: 'Yan APC 2,000 sun koma PDP a jihar Neja

Legit.ng Hausa haka zalika kuwa kamar yadda muka samu shine laifin sa shine na mallaka tare da anfani da takardar shaida watau Satifiket din boge na hukumar shirya jarabawa ma 'yan yammacin Afrika ta kammala karatun Sakandire watau WAEC.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ta na aiki ba dare-ba rana don ganin ta soma biyan mafi karancin albashi na Naira dubu 30 nan ba da dadewa, kamar dai yadda Sakataren gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha ya fada.

Mista Mustapha mun samu cewa ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata a lokacin da yake tsokaci a wajen taron goganni-in-goge ka karo na 25 da hukumar kayyade albashin ma'aikata watau national salaries, incomes and wages commission (NSIWC) ta shirya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel