Kungiyar 'Kwadago ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

Kungiyar 'Kwadago ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

Rahotanni da ke zuwa mana da duminsu da sanadin kamfanin dillancin labarai na kasa sun ruwaito cewa, kungiyar kwadago ta Najeriya, ta sake gindaya wani sabon gargadi na jan kunne ga gwamnatin tarayya tare da shimfida wa'adin daukar mataki.

A jiya Alhamis, Kungiyar kwadago ta Najeriya, ta gindaya gargadi na karshe tare da shimfida wa'adi zuwa ranar 31 ga watan Dasumba, akan gwamnatin tarayya ta gaggauta mika binciken kwamitin sabon mafi karancin albashin ma'aikata na N30, 000 zuwa ga ga majalisara tarayya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, kungiyoyin uku na kwadago da suka yanke wannan hukunci bayan zaman da suka gudanar jiya a birnin Legas sun hadar da; Nigerian Labour Congress (NLC), Trade Union Congress (TUC) da kuma United Labour Congress (ULC).

Kungiyoyi sun yi gargadi kai tsaye shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan ya gaggauta cika alkawarin sa biyo bayan kwamitin da ya kafa na aiwatar a binciken tsare-tsare na fara biyan mafi karancin albashin ma'aikata a kasar nan ba tare an nemi bashi daga wata kafa ba.

Kungiyar 'Kwadago ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya

Kungiyar 'Kwadago ta nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta fara biyan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya
Source: Depositphotos

Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Ayuba Wabba, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawarsa da manema labarai bayan zaman tattaunawa da suka gudanar. Ya ce kafa kwamitin Buhari ba zai zamto wani sharadi na fara biyan mafi karanci albashi ga ma'aikatan kasar nan ba.

KARANTA KUMA: Yadda gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi suka kasafta kudin shiga na watan Nuwamba

Ya kara da cewa, biyan mafi karancin albashi ga ma'aikatan kowace kasa karbabbiyar doka ce da ta karade dukkanin kasashen duniya. Ya buga misali dangane da yadda wasu kasashen nahiyyar Afirka kamar Ghana, Kenya da kuma kasar Afirka ta Kudu suka kara mafi karancin albashin ma'aikatan su a wannan shekara.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buahri ya ziyarci birnin Kanon Dabo domin kaddamar da wasu sabbin ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala tare da halartar bikin yaye sabbin jami'an tsaro na 'yan sanda a kwalejin su da ke garin Wudil.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel