Da wayo, shugaba Buhari ya dawo da tallafin mai, bayan yaga uwar bari

Da wayo, shugaba Buhari ya dawo da tallafin mai, bayan yaga uwar bari

- Naira biliyan 305 aka saka a matsayin tallafin mai a kasafin kudin 2019

- Gwamnatin Buhari dama ta janye tallafin mai a 2016

- An janye tallafin man fetur din ne saboda kalubalen tattalin arziki

assu strike

assu strike
Source: Depositphotos

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar laraba yace Naira biliyan 305 aka saka a matsayin tallafin man fetur a kasafin kudin 2019.

Mista Buhari ya sanar da hakan ne a lokacin da yake bayyana kasafin kudin 2019 ga majalisun wakilai da na tarayya a Abuja.

Da wayo, shugaba Buhari ya dawo da tallafin mai, bayan yaga uwar bari

Da wayo, shugaba Buhari ya dawo da tallafin mai, bayan yaga uwar bari
Source: Depositphotos

Idan zamu tuna gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2016 ta janye tallafin man fetur, hakan ya tirsasa yan kasuwar mai masu zaman kansu janyewa daga shigo da man fetur din.

Janyewar tasu ta bar matatar man fetur ta kasa da alhakin shigo da fetur. Kudin shigo dashi Naira 185 amma na siyarwa a nan kasar Naira 145. Tun daga nan matatar man fetur ta kasa ta fara janyewa daga NLNG, don samar da kudin da suka fadi na kusan Naira 40 a duk lita daya.

Da wayo, shugaba Buhari ya dawo da tallafin mai, bayan yaga uwar bari

Da wayo, shugaba Buhari ya dawo da tallafin mai, bayan yaga uwar bari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: An kammala kashi daya na jirgin kasan da zai taso daga Legas har zuwa Daura

A halin yanzu, matatar man fetur ta kasa ta samu nakasun dala biliyan 1.05 ko Naira biliyan 320 don cike faduwar da akayi,kamar yanda babban daraktan matatar, Mista Maikanti Baru ya sanar.

"Bari inyi amfani da wannan damar gurin bayani akan faduwar da ake a man fetur. A lokacin kalubale na tattalin arziki, dole mu ragewa yan Najeriya nauyi, " inji shi.

Amma kuma hakan ya jawo fushin majalisa, wadanda suka yarda cewa kamfanin man fetur din bashi da hurumin kashe makuden kudaden nan ba tare da yardar majalisar dattawa ba.

Kamar yanda masu kiyasi suka ce, samar da tallafin mai a kiyasin kashe kudin 2019 zai kwantar da tarzoma tsakanin mahukuntan da matatar man fetur ta kasa.

Mista Buhari yace matsalar tallafin mai a baya ana amfani da ita ta yanda bai dace ba kuma ana samun matsalar rashawa ta bangaren yan kasuwar mai masu zaman kansu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel