Akan daidai Buhari yake wajen nada kwamiti kan karin albashi, saboda hauhawar farashi - Masana

Akan daidai Buhari yake wajen nada kwamiti kan karin albashi, saboda hauhawar farashi - Masana

- Yunkurin kafa kwamitin tabbatar da karancin albashi da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, yayi ne don gujewa abinda zai yi ya zuwa ya dawo tsakanin gwamnatocin jihohi da tarayya

- Kwamitin zai kara duba don rage hauhawar farashin kaya

- Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin mika kasafin kudin 2019

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka

A gaskiya PDP na sanya ma'aikatanmu cikin hadari - INEC ta koka
Source: Depositphotos

Dan siyasa, masanin tattalin arziki, Ismaila Suleiman, yace yanke shawarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi na hada kwamitin fasaha don duba tabbatar da sabon karancin albashi a kasar don gujewa hatsaniya ne tsakanin gwamnatocin jihohi da tarayya ne.

Mista Suleiman, wanda ya fadi hakan a ranar laraba a tattaunawar waya tsakanin shi da manema labarai a Abuja, yace shugaban kasar yana sane da irin abinda da yanke shawarar shi zatayi ga matasa marasa aikin yi a matakin jiha.

Akan daidai Buhari yake wajen nada kwamiti kan karin albashi, saboda hauhawar farashi - Masana

Akan daidai Buhari yake wajen nada kwamiti kan karin albashi, saboda hauhawar farashi - Masana
Source: UGC

Kamar yanda yace, shugaban kasar ya yanke shawara mai kyau ta kafa kwamitin duba yanda za'a tabbatar da sabon karancin albashin don ganin bai kara wani nauyin kudi ga wasu jihohin da suke son tabbatar da sabon karancin albashin.

Ya shawarci gwamnatocin jihohi da kada suyi amfani da sabon karancin albashin gurin kin daukar sababbin ma'aikata a jihohin su.

DUBA WANNAN: An zagaye APC a jihar Obasanjo: Dan takarar da gwamnan APC ya tsayar a wata jam'iyyar ya tasamma lashe zabe

Idan zamu tuna, Buhari ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba zai tura tabbatar da sabon karancin albashi ga majalisar dattawa don amincewa.

Mista Buhari ya fadi hakan ne a yayin mika kasafin kudin 2019 na Naira tiriliyan 8.8 ga majalisa.

Ya tabbatar da cewa yana da burin kawo karshen cece ku ce akan karancin albashin, cewa da ya umarci da a kafa kwamitin fasaha da zai duba yanda za'a tabbatar da karancin albashin.

Mista Buhari yace hakan zai kawo karancin tashin kudin kaya Idan aka tabbatar da karancin albashin tare da hana rasa aiyukan yi.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel