Babban kamu: 'Yan APC 2,000 sun koma PDP a wata jiha a Arewa

Babban kamu: 'Yan APC 2,000 sun koma PDP a wata jiha a Arewa

A yayin da babban zaben 2019 ke cigaba da kusantowa, jama'iyar adawa ta PDP ta himmatu wurin ganin ta yi raraka da tsamar nama ga jama'iyar APC mai mulki a Jihar Neja.

Babban jama'iyar adawa ta PDP ta yi babban kamu a Jihar Neja inda ta karbi 'ya'yan jama'iya mai mulki da ADP sama da dubu biyu wadanda suka sauya sheka zuwa jama'iyar ta PDP.

Babban kamu: 'Yan APC 2,000 sun koma PDP a wata jiha a Arewa

Babban kamu: 'Yan APC 2,000 sun koma PDP a wata jiha a Arewa
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Wani jami'in gwamnatin Buhari yayi murabus

Tsohon gwamnan Jihar ta Neja kuma jagoran jama'iyar a Jihar Dr.Mu'azu Babangida Aliyu (Talban Minna) ne ya karbi masu sauya shekar a jiya laraba a garin Bida a lokacin da jama'iyar ke kaddamar da yakin neman zaben dan takarar ta na gwamna.

Alhaji Kudu Kasim shiya jagoranci 'ya'yan jama'iyar ta APC zuwa PDP yayin da Alhaji Muhammad Yahaya (Designer) ya jagorancin mambobin ADP zuwa PDP.

Da yake bayani a yayin taron, Babangida Aliyu ya baiyana cewar "'Yan Najeriya sunga banbanci na zahiri tsakanin jama'iyar APC wacce ta kwashe shekara uku da rabi ba tare da samar da wani tartibin canji ba, yanzu lokaci ne da 'yan Najeriya zasu yi wa kansu zabi na gari a 2019. "Zaben APC yana nufin zuwa matikin talauci na gaba-inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel