Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi

Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi

- Dakarun soji suka yi nasarar dakile wani harin kunar bakin wake da wata mata tayi niyyar kaiwa a yankin Mushimari a karamar Konduga a jihar Borno

- Aisha Modu, 'yar kunar bakin waken, ta cilla jigidar bam dinta cikin ruwa bayan ta hango dakarun soji na zuwa

- Yanzu dai dakarun sojin sun yi nasarar tsamo jigidar da Aisha ta wulla cikin tafkin

A jiya ne dakarun soji suka yi nasarar dakile wani harin kunar bakin wake da wata mata tayi niyyar kaiwa a yankin Mushimari a karamar Konduga a jihar Borno.

'Yar kunar bakin wake, Aisha Modu, ta cilla jigidar bam dinta cikin ruwa bayan ta hango dakarun soji na zuwa.

Yanzu dai dakarun sojin sun yi nasarar tsamo jigidar da Aisha ta wulla cikin tafkin, kamr yadda zaku iya gani a cikin hotuna.

Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi

Dakarun soji sun tsamo jigidar bam
Source: UGC

Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi

Jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi
Source: UGC

Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi

Dakarun soji sun tsamo jigidar bam da 'yar kunar bakin wake ta jefa cikin kududdufi
Source: UGC

Ko a jiya, Laraba 19 ga watan Disambar 2018, jami'an sojin Najeriya sun yi nasarar kama wata 'yar kunan bakin wake tare da mai taimaka mata a garin Mushirmari a karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Hukumar soji ta yiwa Janar 5 ritaya

Sanarwar da hukumar sojin ta fitar ta shafinta na Twitter ya ce an kama su ne yayin da suke kokarin ratsa inda battaliyar soji ta 222 ke tsarewa.

An kama ta sanye da rigar bam a jikinta kuma anyi nasarar warware bam din ba tare da ya tashi. Ana cigaba da zurfafa bincike a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel