Da dumin sa: Wani babban jami'in gwamnatin Buhari yayi murabus daga mukamin sa

Da dumin sa: Wani babban jami'in gwamnatin Buhari yayi murabus daga mukamin sa

Wani daga cikin mukarraban gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kuma shugaban hukumar gudanarwar Ma'aikatar dake da alhakin samarwa tare da tabbatar da zaman lafiya da kuma sasanci a tsakanin 'yan kasar Najeriya watau Institute for Peace and Conflict Resolution a turance yayi murabus.

Shugaban hukumar gudanarwar watau Governing Council a turance, Sanata Muhammed Abba-Aji din dai ya gabatar da takardar murabus din sa ne ga sauran 'yan hukumar gudanarwar a ranar Alhamis.

Da dumin sa: Wani babban jami'in gwamnatin Buhari yayi murabus daga mukamin sa

Da dumin sa: Wani babban jami'in gwamnatin Buhari yayi murabus daga mukamin sa
Source: Twitter

KU KARANTA: Abu 5 da za ku sani game da Marigayi Alex Badeh

Mai magana da yawun Ma'aikatar, Mista Abu Michael ne ya sanarwa da manema labarai hakan a cikin wata takarda da ya raba masu dauke da sa hannun sa.

Legit.ng Hausa ta samu cewa Shi dai Sanata Muhammed Abba Aji a baya ya nemi tikitin takarar gwamnan jihar Borno ne a karkashin jam'iyyar APC ama sai bai samu nasara ba kuma yanzu shine ya samu tikitin takarar kujerar Sanata a jam'iyyar PDP.

A wani labarin kuma, Karamin ministan albarkatun man fetur na kasar Najeriya Mista Ibe Kachikwu ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari har yanzu bata zuba ko da kwandalar ta ba a cikin matatun man fetur din kasar nan.

A cewar Ministan, wannan ko shakka babu wata nasara ce da gwamnatin ta samu amma wadda al'ummar kasa ba su maida hankali a kai ba musamman idan aka yi la'akari da gwamnatocin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel