Kannywood da siyasa: Maryam Booth tayi murabus daga shugabancin gidauniyar Atiku

Kannywood da siyasa: Maryam Booth tayi murabus daga shugabancin gidauniyar Atiku

Shahrarriyar jarumar fina-finan Hausa, Maryam Booth, ta yi murabus daga kujerar mataimakiyar shugabar gidauniyar dan takaran shugaban kasa, Atiku Abubakar daga ranan Litinin, 24 ga watan Nuwamba, 2018.

Jarumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram @officialmaryambooth cewa daga ranan 24 ga wata, ba ta son wannan kujera da dan siyasan.

A cewarta: "Ina son sanar da murabus dina a matsayin mataimakiyar shugabar gidauniyar Atiku daga ranan 24 ga watan Disamba, 2014."

Nagode da daman da aka bani na watanni hudu da suka gabata, nagode da goyon bayan da aka bani. Na ji dadin lokacin da nayi tare da giduniyar kuma ina matukar godiya,"

KU KARANTA: Yan majalisan dattawa sun tafi hutu sai sabuwar shekara

Atiku Abubakar ne dan takaran kujeran shugaban kasan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a zaben 2019.

A kwanakin, rahotanni sun bayyana cewa an samu rabuwar kai a cikin masana'antar Kannywood tsakanin Atiku Abubakar na PDP da shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressive Congress, APC.

Tuni manya a masana'antar Kannywood sun bayyana wadanda zasu marawa baya a zaben 2019. Yayinda jarumi Ali Nuhu Mohammed ya alanta cewa shugaba buhari zai yi, jarumi Sani Musa Danja ya ce su dai Atiku zasuyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel