Buhari yayi ganawar sirri da wasu makusantan Kwankwaso 5

Buhari yayi ganawar sirri da wasu makusantan Kwankwaso 5

A daren Larabar da ta gabata ne dai Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya gana da wasu mukarraban tafiyar Kwankwasiyya kuma makusantan tsohon gwamnan jihar Kano, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso a wani mataki na komawar su jam'iyyar APC daga PDP.

Kamar yadda muka samu, mukarraban tsohon gwamnan wadanda kuma suma 'yan siyasa ne da Shugaba Buhari ya tattauna da su sun hada da tsohon mataimakin gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar.

Buhari yayi ganawar sirri da wasu makusantan Kwankwaso 5

Buhari yayi ganawar sirri da wasu makusantan Kwankwaso 5
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Tsohon gwamnan PDP ya shirya komawa APC

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa sauran sun hada da tsohon ma'aji na jam'iyyar APC a mataki na tarayya watau Bala Gwagwarwa da kuma tsohon shugaban hukumar nan dake kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya watau Nigerian Ports Authority (NPA) a turance, Aminu Dabo.

Cikon na hudu da na biyar din da shugaba Buhari ya tattauna da su din kamar yadda muka samu su ne Injiniya Muazu Magaji da kuma Isa Zarewa wadanda aka ce dukkan su mukarraban darikar kwankwasiyya ne.

Idan dai har hakan ta faru to kau lallai masana siyasa na ganin cewa shugaban kasar a iya cewa ya karya lagon Sanata Kwankwaso din a siyasance a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel