Yiwa Shugaba Buhari Ihu a zauren Majalisa rashin tarbiya ce tsagwaranta - Gwamna Bello

Yiwa Shugaba Buhari Ihu a zauren Majalisa rashin tarbiya ce tsagwaranta - Gwamna Bello

Daya daga cikin gwamnonin Arewa watau Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, ya yi raddi ga wasu 'yan majalisar tarayyar Najeriya, dangane da ihun da suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba yayin gabatar da kasafin kudin kasa na 2019.

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya kaca-kaca da wasu Sanatoci da kuma mambobin Majalisar wakilan Najeriya, dangane da ihun da suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Laraba cikin zauren Majalisar tarayya yayin gabatar da kasafin kudin kasa na shekarar badi.

Ko shakka ba bu wasu 'yan majalisar sun rinka ihu domin nuna adawa dangane da wasu bayanai na shugaba Buhari, yayin da wasu suka rinka sowa domin nuna goyon bayan a gare sa.

Yiwa Shugaba Buhari Ihu a zauren Majalisa rashin tarbiya ce tsagwaranta - Gwamna Bello

Yiwa Shugaba Buhari Ihu a zauren Majalisa rashin tarbiya ce tsagwaranta - Gwamna Bello
Source: Twitter

Gwamna Bello, yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya, ya fede Biri har wutsiya ga 'yan majalisar da suka yiwa shugaban kasa ihu na adawa. Bello ya ce sun gaza samun tarbiyar ne tun daga tsatson iyayen su.

Ya ce, ba bu dace dangane da wannan cin fuska da 'yan Majalisar suka yiwa shugaba Buhari, kasancewar sa mutum mai dattako da kuma tsantsar kishin kasar nan da mamaye zuciyarsa wajen tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya domin al'ummar Najeriya su sharba har su gyatse.

KARANTA KUMA: Walƙiya ta kashe wata Uwa da 'ya'yan ta 2 a ƙasar Malawi

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugabannin majalisun biyu; Abubakar Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara, sun yi iyaka bakin kokarin su na ladabtar da 'yan majalisar yayin wannan lamari da duniya ta ganewa idanun ta.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, jam'iyyar APC ta yi raddi dangane da wannan lamari, inda ta ce za ta ramawa kura aniyyarta, ta hanyar fadakar da al'ummar kasar nan wajen kauracewa zaben wadanda suka yiwa shugaba Buhari tsaurin idanu a zauren majalisar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel