Idonka ya rufe da son mulkin Najeriya - Gwamnatin tarayya ta caccaki Atiku

Idonka ya rufe da son mulkin Najeriya - Gwamnatin tarayya ta caccaki Atiku

- Gwamnatin tarayya ta bayyana tsananin son mulkin Najeriya a matsayin abunda ke damun Atiku

- Ta bayyana cewa hakan ne yasa shi cewa za’a ci gaba da kashe-kashe idan har aka sake zabar

- Ministan labarai ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya daina kazamiyar siyaa sannan ya daina siyasantar da kashe-kashe

Gwamnatin tarayya ta bayyana tsananin son mulkin Najeriya a matsayin dalilin da yasa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar cewa za’a ci gaba da kashe-kashe idan har aka sake zabar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ministan labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana matsayar gwamnati a wani taron labarai a ranar Alhamis, 20 ga watan Disamba a Abuja.

Idonka ya rufe da son mulkin Najeriya - Gwamnatin tarayya ta caccaki Atiku

Idonka ya rufe da son mulkin Najeriya - Gwamnatin tarayya ta caccaki Atiku
Source: Depositphotos

Ministan ya bayyana cewa Atiku ya matsu da yawa sannan ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya daina kazamiyar siyaa sannan ya daina siyasantar da kashe-kashe.

Ministan ya kuma yi martani ga zargin da jama’a ke yi akan sake kama tare da tsare Deji Adeyanju.

KU KARANTA KUMA: Albashi: Ba mu yarda Buhari ya gindaya sharudda kafin ya yi kari ba – Kungiyar Kwadago

Mohammed ya bayyana cewa zargin da ake na tsoron cewa hukumomin tsaro na iya tsunduma siyasa a lokacin zaben 2019 a matsayin hasashen yan adawa.

Ministan ya kuma bayar da tabbacin cewa a karkashin idanun Buhari, babu hukumar tsaro da zata aikata irin hakan a kowani zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel