Abinda Buhari ya kamata ya yi bayan 'yan majalisa sun yi masa ihu - Atiku

Abinda Buhari ya kamata ya yi bayan 'yan majalisa sun yi masa ihu - Atiku

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuawar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya yi murabus bayan abinda ya faru tsakaninsa da 'yan majalisa yayin da yaje gabatar da kasafin shekarar 2019 a jiya, Laraba.

Atiku ya ce idan haka ta faru a kasashen da ake da cigaba, shugaban kasa ba zai bata lokaci wajen mika takardarsa ta yin murabus ba.

Dan takarar shugaban kasar ya yi wannan furuci ne a cikin wani jawabi da Ambasada Aliyu Bin Abbas, mai bayar da shawara na musamman a uwar kungiyar masoya Atiku ta kasa (Atiku Support Groups).

Jawabin ya ce, "ihun da 'yan majalisar suka yiwa Buhari alama ce dake nuna cewar basu gamsu da salon mulkinsa ba saboda gazawar gwamnatinsa.

Abinda Buhari ya kamata ya yi bayan 'yan majalisa sun yi masa ihu - Atiku

Atiku
Source: Depositphotos

"Tunda mafi yawan mambobin majalisa basu amince da shi ba, abinda yafi sauki gare shi shine ya yi murabus ba yake yi masu tunin cewar duniya na kallon abinda suke yi ba."

A jiya ne Legit.ng ta kawo maku labarin cewar wasu mambobin majalisar wakilai suka yiwa shugaba Buhari ihu yayin da ya isa zauren majalisar domin gabatar da kasafin kudin shekarar 2019.

Daya daga cikin mambobin majalisar wakilai 'yan jam'iyyar PDP ya bayyana cewar sun yiwa shugaba Buhari ihu ne domin nuna rashin jin dadinsu bisa yadda gwamnatin tarayya ta gaza yin aiki da kasafin kudin shekarar 2018 kamar yadda ta gabatar.

DUBA WANNAN: Atiku ya yiwa Buhari gori a kan karuwar marasa aiki a Najeriya

Da shigar Shugaba Buhari zauren majalisar sai wasu mambobi suka kaure da ihun "noooo", "noooo" tare da yin ihun "karyane", "karyane" lokacin da Buhari ya fara zayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu.

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala gabatar da kasafin, shugaban wata kungiyar 'yan majalisar tarayya Jam'iyyar PDP, Chukwuma Onyema, ya bayyana rashin jin dadin 'yan majalisar a kan yadda bangaren zartarwa ke nuna son a kai wajen zabar aiyukan da zata kaddamar daga cikin wadanda ta gabatar a kasafinta na shekarar 2018.

Kazalika, ya bayyana cewar hatta yajin aikin da ma'aikatan majalisar ke yi na da alaka da rashin kaddamar da kasafin kudin shekarar 2018.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel