Wata mata ta kaiwa 'yan sanda biyu farmaki da fasashiyar kwalba

Wata mata ta kaiwa 'yan sanda biyu farmaki da fasashiyar kwalba

An gurfanar da wata mai treda, Modinat Adebayo a gaban kotun majistare da ke Ikeja bisa zarginta da jiwa jami'an 'yan sanda biyu rauni da fasasun kwalabe.

Ana tuhumar Modinat da ke zaune a gida mau lamba 25 Koya Akinwale Street., Baruwa-Ipaja Legas da laifin hadin baki da raunata 'yan sanda.

Mai shigar da karar, Inspecta Rachael Williams ta shaidawa kotu cewa wanda ake zargin ta yiwa Saja Ngbede Ichigboja da kofur Folajimi Adeniyi rauni da fasasun kwalabe da kwanuka.

Williams ta ce Adebayo tayi musu rauni a kawunnansu.

Wata mata ta kaiwa 'yan sanda biyu farmaki da fasashiyar kwalba

Wata mata ta kaiwa 'yan sanda biyu farmaki da fasashiyar kwalba
Source: Facebook

Ta kara da cewa wanda ake zargin ta aikata laifin ne tare da dan ta Ismaila da wasu yara a ranar 15 ga watan Disamba a gida mai lamba 25 Koya Akinwale Street, Baruwa-Ipaja a jihar Legas.

DUBA WANNAN: 'Yan siyasar Najeriya basu iya dimokuradiyya ba sam - Farfesa Yakubu

Williams ta ce 'yan sandan suna sintirinsu ne lokacin da abin ya faru.

Ta kara da cew wanda ake zargin ta hana 'yan sandan daukan matakin da doka ya tanadar ta hanyar boye yaron ta da wasu yaran da ya dace a kama.

"Yan sandan suna wucewa a cikin motarsu ne kwatsam sai aka fara jifansu da fasasun kwalabe da da kwanuka. Yan sandan ba kame suka je ba, kawai suna wucewa ne yayin da abin ya faru.

"Daga baya 'yan sandan sun gano yaron wanda ake tuhumar yana shan tabar wiwi ne da abokansa hakan yasa su kayi tsamanin an zo kama su ne," inji Williams.

Ta ce laifin ya sabawa sashi na 173 da 411 na dokar masu laifi na jihar Legas na shekarar 2015.

Sai dai bayan an karanto karar, wadda ake tuhumar ta musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Mrs O.O. Akingbetese ta bayar da belin Adebayo kan kudi N200,000 kuma ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Janairun 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel