Hanyoyin da yajin aikin ASUU zai kawo cikas ga zaben 2019 - INEC

Hanyoyin da yajin aikin ASUU zai kawo cikas ga zaben 2019 - INEC

- INEC ta bayyana cewa tana jin tsoron yajin aikin da kungiyar ASUU ke ci gaba da gudnarwa a kasar zai jawo babba cikas ga zaben 2019

- Hukumar ta bayyana cewa kusan kashi 70 cikin sama da mutane miliyan daya da take dauka aikin zaben, tana samunsu ne daga dalibai da malaman jami'o'in

- Da wannan ne ya sa hukumar ta bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU da su cimma wata matsaya ta kawo karshen yajin aikin kafin wata daya da zabe

Hukumar zabe mai zama kanta ta kasa (INEC), ta ce yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) suke gudanarwa a fadin kasar, zai kawo babban nakasu ga shirye shiryen hukumar na gudanar da babban zabe na 2019.

Mr Festus Okoye, shugaban kwamitin watsa labarai da ilimi kan kad'a kuri'a na INEC, ya bayyana hakan a Abuja a wani taron wayar da kai na masu ruwa da tsaki kan watsa labarai da kuma muhimmancin banbancin jinsi a wajen watsa labarai na harkokin zabe.

A cewar Okoye, ko kusa mambobin matasa masu yiwa kasa hidima NYSC, ba zasu iya samar da adadin ma'aikatan da hukumar ke bukata ba, don gudanar da aikin zaben.

KARANTA WANNAN: Gaskiyar Magana: Soyayyar Buhari ga 'yan Nigeria bata misaltuwa - Osinbajo

Maganar Gaskiya: Yajin aikin ASUU zai kawo babban cikas ga zaben 2019 - INEC

Maganar Gaskiya: Yajin aikin ASUU zai kawo babban cikas ga zaben 2019 - INEC
Source: Depositphotos

Ya ce kusan kashi 70 na jami'an zaben da ake amfani da su a jihohin fadin kasar, ana dauko su ne daga daliban jami'o'in kasar.

"Akan zaben 2019, INEC zata dauki sama da ma'aikata miliyan daya, wadanda suka hada da malaman jami'o'i, da kuma dalibai na jami'o'in kasar, tare da matasa masu yiwa ksa hidima. Don haka yana da muhimmanci ace an janye yajin aikin wata daya kafin fara zaben, ma damar ana son zaben ya gudana bisa tsari," a cewarsa.

Don haka Okoye ya bukaci kungiyar ASUU da gwamnatin tarayya da su gaggauta cimma wata matsaya da zata warware wannan yajin aikin da ake yi, wanda ya haddasa rashin tabbas akan fannin ilimi na kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel