Ban goyi bayan rashin sakin Dasuki da Buhari da gwamnatin tarayya suka ki yi ba – Malami ga kotu

Ban goyi bayan rashin sakin Dasuki da Buhari da gwamnatin tarayya suka ki yi ba – Malami ga kotu

- Ministan shari’a, Mista Abubakar Malami ya karyata goyon bayan gwamnatin tarayya wajen yin watsi da umurnin kotu sau shida akan sakin Dasuki

- Gwamnati dai taki sakin tsohon mai ba kasa shawara akan tsaro, Kanal Sambo Dasuki duk da umurnin kotu

- Malami ya kuma yi ikirarin cewa babu wani abun gabatarwa a kotu da zai nuna cewa Dasuki ya cike dukkanin ka’idojin belin da aka basa

Babban alkalin Najeriya kuma ministan shari’a, Mista Abubakar Malami ya karyata goyon bayan gwamnatin tarayya wajen yin watsi da umurnin kotu sau shida inda ta yi umurnin bayar da beli ga tsohon mai ba kasa shawara akan tsaro, Kanal Sambo Dasuki wanda ke tsare.

Ban goyi bayan rashin sakin Dasuki da Buhari da gwamnatin tarayya suka ki yi ba – Malami ga kotu

Ban goyi bayan rashin sakin Dasuki da Buhari da gwamnatin tarayya suka ki yi ba – Malami ga kotu
Source: Depositphotos

Malami ya bayyana hakan a wani takardar rantsuwa da ya cike a gaban kotu, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yan ace kan cewa lallai zargin da ake na cewa ya marawa gwamnatin tarayya baya akan abunda take yiwa Dasuki karya ne, yace an shirya shi ne don kawai asa duniya tayi masa dariya.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyun siyasa na neman a basu kudi don su amince da Buhari – Oshiomhole

Ya kuma yi ikirarin cewa babu wani abun gabatarwa a kotu da zai nuna cewa Dasuki ya cike dukkanin ka’idojin belin da aka basa a ranar 2 ga watan Yuli, 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel