An kammala kashi daya na jirgin kasan da zai taso daga Legas har zuwa Daura

An kammala kashi daya na jirgin kasan da zai taso daga Legas har zuwa Daura

- Ministan sufuri ya gwada titin jirgin kasa mai kilometers 32

- Titin ya fara daga Legas zuwa Ibadan

- Muna godiya ga yan kasar China da irin wannan fasahar amma lokaci yayi muma da zamu fara yin gadojin mu da kanmu

An kammala kashi daya na jirgin kasan da zai taso daga Legas har zuwa Daura

An kammala kashi daya na jirgin kasan da zai taso daga Legas har zuwa Daura
Source: Depositphotos

Ministan sufuri, Rt. Hon. Rotimi Amaechi a ranar talata, tare da yan kwamitin sufuri na majalisar wakilai sun kammala zagayen titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan da aka kammala.

Ministan sufurin ya tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da wasu ministoci zasu hau jirgin kasa daga Iju a Legas zuwa Abeokuta a jihar Ogun a makon farko na watan Janairu na 2019.

Da yayi magana da yan jarida a ranar talata a Abeokuta bayan kammala duba titin jirgin, da farinciki yayi godiya ga kowa da aka fara gyaran titin jirgin dashi.

Kamar yanda ministan sufurin yace, "Zaku tuna lokacin da aka fara aikin, gurin babban daji ne. Amma yanzu akwai gadoji da suka tsallake ruwan da muke amfani dasu wajen wucewa. Muna godiya ga China da irin fasahar su, amma lokaci yayi da ya kamata mu fara titunan mu da gadojin mu da kanmu. Wasu kasashe nayi, bazamu cigaba da dogara da wasu mutanen gurin cigaban kasar mu ba. "

DUBA WANNAN: Abuja-Kaduna Rail Services: Lokutan tashin jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna a ranakun litinin zuwa asabar

"A yau, ina godiya gareku kafofin yada labarai akan irin kokarin ku tun daga fara aikin nan. So da yawa lokacin duba aikin, motocin manema labarai kan lalace kuma mu bar su akan. Inaso in mika godiya ga duk manema labarai akan sadaukarwar da sukayi akan aikin nan."

"A hankali muke kawowa karshen aikin nan. Kilometers 6 kenan da muka bar Abeokuta kuma na tabbatar cewa zuwa satin farko na watan Janairu na 2019, mataimakin shugaban kasa da wasu ministoci zasu hau jirgin kasa daga Iju zuwa Abeokuta. Bayan nan ne za'a fara daukar fasinjojin. Daga nan zamu takura yan kwangilar dasu gida tashoshin jirgin."

"Ina so in mika godiya ta ga majalisar wakilai da suka taya duba aiyukan a yau. Idan yan kwangilar suka cigaba da aiki kamar yanda suke yi yanzu, zamu kai har Ibadan a karshen watan Janairu.

"

"Nan ba da dadewa ba zamu kiyasin kudaden da aikin yaci mu mika shi ga BPP don aikin da ya dace. Abubuwan da yaci wadanda ba a kiyasta dashi ba ya hada da rush barikin sojoji na Yaba, Legas, rusassun gine gine a Abeokuta da sauran su," Amaechi ya kara da hakan.

Shugaban kwamitin majalisar akan sufuri, Abdulmumin Jibrin, ya jinjiinawa mai girma ministan sufuri akan aiyukan da ya jagoranta. A kalaman shi, "Da abinda muka gani a yau, muna jinjiinawa ministan akan aikin da yayi. Abu daya ne abin haushi na a yau shine, duk aiyukan nan da suka kammala da nasarorin nan da aka samu ba a a kawo rahoton su yanda ya dace."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel