Albashi: Ba mu yarda Buhari ya gindaya sharudda kafin ya yi kari ba – Kungiyar Kwadago

Albashi: Ba mu yarda Buhari ya gindaya sharudda kafin ya yi kari ba – Kungiyar Kwadago

- Kungiyar Kwadago ta yi watsi da furucin da Buhari na cewa zai amince da karin albashin ma’aika, amma sai an sake nazari kan batutuwan da ka iya tasowa bayan karin albashin

- Sun ce ba za su yarda da duk wani bincike-bincike da kwakule-kwakulen yadda za a nemo mafita a nan gaba kamar yarda Buhari ya yi bayani ba

- Buhari dai yayi jawabi kan Karin albashin ne yayin da ya gabatar da kasafin kudin 2019

Kungiyar Kwadago ta Najeriya, ta yi watsi da furucin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na cewa zai amince da karin albashin ma’aika, amma sai an sake nazari kan batutuwan da ka iya tasowa bayan karin albashin.

A jiya Laraba, 19 ga watan Disamba ne dai shugaban kasar ya bayyana hakan a jawabin kasafin kudi da ya gabatar a Majalisar dokokin kasar cewa, zai turo da batun karin albashi a majalisa domin a amince ya zama doka nan ba da jimawa ba.

Albashi: Ba mu yarda Buhari ya gindaya sharudda kafin ya yi kari ba – Kungiyar Kwadago

Albashi: Ba mu yarda Buhari ya gindaya sharudda kafin ya yi kari ba – Kungiyar Kwadago
Source: Depositphotos

Sai dai kuma a cikin jawabin na sa, Buhari ya nemi ‘yan majalisa da su bi batun a cikin tsanaki, domin su duba yadda karin albashin ba zai kara tsunduma Najeriya shiga gidaje ko kasashe neman ramcen kudaden da za ta rika biyan albashi a kowane karshen wata ba.

Wannan furuci na Buhari ne shugabannin kungiyar ta kwadago, suka yi wa kakkausar suka.

Sun jaddada cewa su kawai abin da suka sani shi ne, Shugaba Buhari ya sa hannun amincewa cewa naira 30,000 ce mafi kankantar albashi kawai, kuma ya mika wa majalisa ita ma ta amince, shikenan batun ya zama doka.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da nadin sabuwar mai shari'a na kotun koli

Sun ce ba za su yarda da duk wani bincike-bincike da kwakule-kwakulen yadda za a nemo mafita a nan gaba kamar yarda Buhari ya yi bayani ba.

Shugaban Kwadago Ayuba Wabba, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN cewa duk wani sa-toka-sa-katsi da gwamnatin tarayya za ta yi, idan ta sake ta rage ko da naira daya daga cikin naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, to ba za su taba amincewa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel