Walƙiya ta kashe wata Uwa da 'ya'yan ta 2 a ƙasar Malawi

Walƙiya ta kashe wata Uwa da 'ya'yan ta 2 a ƙasar Malawi

Za ku ji cewa, azal ta sanya tartsatsin walƙiya yayin mamakon ruwan sama ya sheƙe wata Uwa tare da 'ya'yayen ta biyu har Lahira a Yammacin kasar Malawi kamar yadda hukumomin tsaro na 'yan sanda suka zayyana a jiya Laraba.

Kaitano Lubrino, kakakin rundunar 'yan sanda na kasar, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai kamar yadda kafar watsa labarai ta Dpa-International ta ruwaito.

Kazalika cikin rahoto guda, walƙiyar ta laso wani Magidanci mai shekaru 41 a duniya, inda shima ya ce ga garin ku nan a ranar Litinin din da ta gabata.

Walƙiya ta kashe wata Uwa da 'ya'yan ta 2 a ƙasar Malawi

Walƙiya ta kashe wata Uwa da 'ya'yan ta 2 a ƙasar Malawi
Source: UGC

Lubrino ya bayyana cewa, Clara Mbewe, mai shekaru 34 a duniya da kuma 'ya'yayen ta biyu Mata masu shekarun haihuwa na 4 da kuma 8, sun riga mu gidan gaskiya yayin da tartsatsin walkiyar ya laso su suna tsaka da gudanar da aikace-aikacen sanwa a dakin dahuwa.

Da yake akwai sauran kwanakin sa a gaba, babban da ga Marigayiya Clara dan shekaru 10 a duniya, na ci gaba da gumurzu domin samun waraka a wata babbar cibiyar lafiya ta kasar Malawi rai a hannun Mai Duka.

KARANTA KUMA: APC ta yi martani kan caccakar Buhari a zauren Majalisa

Majiyar rahoton jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mamakon ruwan sama mai hadi da iska mai karfin gaske da kuma walkiya na ci gaba da kwarara tamkar da bakin kwarya a yankunan kasar ta Malawai da ke Kudu maso Gabashin nahiyyar Afirka.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, walkiya mai hadi da tsawo ta salwantar da rayukan mutane 26 cikin kasar Mozambique da kuma Rwanda a wannan shekara ta 2018 kamar yadda shafin BBC Hausa ya ruwaito.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel