Amurka ta sake aiko kudin gudummawa ta daloli ga jami'an tsaro don zaben 2019

Amurka ta sake aiko kudin gudummawa ta daloli ga jami'an tsaro don zaben 2019

- US ta ba NSCDC kyautar kayan aiki na kimanin dala 100,000

- Kyautatawar zata karfafa aiyukan tsaro a arewa maso gabas

- Kayan tallafin sun hada da janareto KVA guda arba'in, akwatunan taimakon gaggawa da sauran su

Amurka ta sake aiko kudin gudummawa ta daloli ga jami'an tsaro don zaben 2019

Amurka ta sake aiko kudin gudummawa ta daloli ga jami'an tsaro don zaben 2019
Source: Twitter

Kasar Amurka, ta ba NSCDC kyautar kayan aiki na kimanin dala 100,000 don karfafa aiyukan su.

Babban kwamnadan NSCDC, Muhammad Gana ya mika kayan aikin ga hukumar NSCDC reshen jihar Borno a Maiduguri a ranar laraba.

Ahmed Audi, mataimakin shugaban hukumar ne ya wakilci Mista Gana, wanda shine ke da alhakin kula da arewa maso gabas, yace Kyautatawar zata bunkasa aiyukan hukumar.

Ya jaddada maida hankalin NSCDC wajen tsare abubuwan more rayuwa a kasar.

Mista Gana yace hukumar ta tura sama da jami'an ta 1,000 don taimakawa sojoji wajen kawo karshen ta'addanci a arewa maso gabas.

Kamar yanda yace, babban alhakin jami'an shine hana tashin hankali ta hanyoyi da dama.

"Hukumar ta maida hankali gurin cigaban walwalar ma'aikatan ta, kamar yanda ta kara wa ma'aikatan girma kwanan nan," inji shi.

DUBA WANNAN: Hadimul Islama ya tasamma karas da kaba'ira a birnin Kano da kewaye

Mista Gana ya jinjiinawa US da kuma gwamnatin jihar Borno akan tallafin su marasa adadi ga NSCDC, ya kuma hori jami'an dasu maida hankali ta hanyar nuna da'a da jajircewa wajen aiyukan su.

Shugaban INL, James Jewett ya jaddada cewa gwamnatin U.S zata cigaba da taimakawa cibiyoyin tsaro a Najeriya don ganin cigaban tsaro ya tabbata.

"INL tana mutunta dangartakar da muke da ita da NSCDC kuma zamu cigaba da taimaka mata da horarwa tare da kayan aiki, " inji Jewett.

Gwamna Kashim Shettima, ya jinjiinawa U.S akan tallafin da ta bawa hukumar, ya tabbatar da hakan zai taka rawar gani wajen dawo da zaman lafiya a yankin.

Majiyar mu ta gano ce kayan da suka bada tallafin sun hada da janareto KVA guda 40, akwatunan taimakon gaggawa da sauran su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel